Ministan Harkokin Wajen Iran, Abbas Araghchi

Iran ta musanta cewa akwai wata tattaunawa da take yi da Amurka, sakamakon cewar da Shugaba Donald Trump ya yi na cewa za su fara sabon tattaunawa ranar Litinin domin kawo ƙarshen yaƙin su wanda yanzu ya kai tsawon watanni shida.

Wannan ƙaryatawar ta fito ne daga ma’aikatar harkokin wajen Iran, bayan Trump ya ce ya dakatar da kai sabbin hare-hare kan ƙasar Iran domin bayar da dama a war ware matsalar ta hanyar diflomasiyya.

Sai dai ma’aikatar harkokin wajen Iran ta musanta cewa ana yin wata tattaunawa a halin yanzu.

“Ba bu wata tattaunawa tsakanin mu da Amurka a yanzu. Da Oman ce kadai mu ke tattaunawa domin tabbatar da wucewa ta mashigar Hormuz,” in ji kakakin ma’aikatar, Esmaeil Baqaei, a lokacin taron manema labarai na mako-mako.

Washington da Tehran sun fara yaƙi tun 28 ga Fabrairu, inda Amurka da Isra’ila suka kai hare-hare kan Iran.

Makon da ya gabata Trump ya yi barazanar cewa zai kai wa Iran hari “mai ƙarfi sosai”, inda ake cewa Shugaban Amurkan na la’akari da sabbin hare-hare, har da kai hari kan ababen more rayuwa na makamashi.

Amma shugaban ya janye daga wannan barazana ranar Asabar, inda ya ce akwai yiwuwar a cimma yarjejeniya, lamarin da Iran ta ƙaryata.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *