Shugaba Tinubu ya rattaba hannu kan kasafin kudin 2026 na N68.32 trillion. Kashi 50% na kudin zai tafi ne ga manyan ayyuka. Karanta cikakken labarin."

Shugaban Kasa Bola Ahmed Tinubu ya rattaba hannu a kan dokar kasafin kudin shekarar 2026, wanda ya kai jimillar Naira tiriliyan 68.32.

Wannan mataki ya biyo bayan amincewa da kudurin da Majalisar Dokoki ta Kasa ta yi ne cikin gaggawa.

Baya ga sabon kasafin kudin, Shugaban ya kuma sanya hannu kan tsawaita wa’adin aiwatar da wani bangare na kasafin kudin shekarar 2025 daga ranar 31 ga watan Maris zuwa 30 ga watan Yuni, 2026, domin ba da damar kammala manyan ayyukan da aka fara a fadin kasar nan.

Wata sanarwar da Fadar Shugaban Kasa ta fitar ta hannun Mai Ba Da Shawara kan Harkokin Yada Labarai, Bayo Onanuga, ta ce manyan ayyuka za su lashe kashi 50 cikin 100 na kasafin da ya kai Naira tiriliyan 32.2. yayin da aka ware Naira tiriliyan 15.8 domin biyan bashi.

Bangaren gudanarwa zai lashe Naira tiriliyan 15.4, yayin da aka ware Naira tiriliyan 4 da doriya domin ko ta kwana.

Gwamnatin ta  ce tsawaita lokacin aiwatar da kasafin kudi na shekarar da ta gabata zai taimaka wa ma’aikatu da hukumomin gwamnati su kammala manyan ayyukan gina ababen more rayuwa da suke kan matakin kammalawa.

Shugaba Tinubu ya bai wa ma’aikatu da hukumomi umarnin gudanar da ayyukansu bisa nagarta tare da kammala su kan lokaci domin amfanin al’ummar kasa.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *