Jami’an Hukumar Wasanni ta Jihar Legas sun tarbi tawagar Hukumar Ƙwallon Ƙafa ta Afirka (CAF), zuwa Legas, yayin da ake ƙara ƙaimi wajen shirye-shiryen gudanar da taron bayar da Kyaututtukan CAF na 2026.

Gwamnan Jihar Legas, Babajide Sanwo-Olu, shi ne ya tabbatar da hakan a shafin sa na sada zumunta na X, ranar Litinin.

Tawagar wacce ke da alhakin tantance wajen gudanar da taron ta zagaya wuraren da aka tsara za a gudanar da wannan babban bikin na nahiyar, a matsayin wani ɓangare na tsarin aikin ta kafin gudanar da bikin baiwa ‘yan wasa kyaututtuka.

A cewar Gwamnan, jami’ar Hukumar Wasanni ta Jihar Legas ne suka jagoranci tawagar CAF zuwa wurare daban-daban, yayin da suka kuma tattara ra’ayoyinsu kan muhimman abubuwa na shirye-shiryen karɓar bakuncin.

Hukumar Wasanni ta Legas ta jaddada cewa karɓar bakuncin biki mai girma kamar taron bayar da Kyaututtukan CAF yana buƙatar tsare-tsare na musamman, inda ake duba kowane daki-daki domin tabbatar da gudanar da shi cikin nasara.

“Mun jagorance su zuwa wuraren kuma mun tattara ra’ayoyinsu, ” in ji Hukumar.

Wannan ziyara ta duba wurare alama ce ta wani muhimmin mataki a cikin shirye-shiryen Legas, yayin da birnin ke ƙoƙarin gudanar da ɗaya daga cikin manyan bukukuwa na shekara-shekara a ƙwallon ƙafar Afirka cikin nasara.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *