Screenshot

Rundunar ‘Yan Sandan Babban Birnin Tarayya (FCT) ta kwato bindigogi kirar FN FAL guda biyu da kuma alburusai bayan kai wani samame a maboyar wasu da ake zargi da aikata laifukan ta’addanci a Dajin Madam.

A cewar rundunar, samamen ya biyo bayan ci gaba da bincike kan kama wasu mutane hudu da ake zargi da samar da makamai, alburusai da miyagun kwayoyi ga ‘yan fashi daji.

Rundunar ta bayyana cewa jami’an sashen yaki da Garkuwa da Mutane na rundunar sun gudanar da aikin ne a ranar 2 ga Agusta, 2026, bayan samun sahihin bayanan sirri.

Ta ce bayanan sun kai jami’an zuwa Dajin Madam, yankin da ke tsakanin jihohin Filato da Bauchi, inda aka gano cewa kungiyar masu aikata laifukan na amfani da wajen a matsayin maboya.

Binciken rundunar ya nuna cewa Musbahu Ishaq na karbar makamai da alburusai daga hannun wani Rabiu Hassan, sannan ya rika kai su ga wani Baba Alhaji Sanusi, wanda ake zargi da jagorantar ‘yan fashi daji kuma har yanzu yana gudun hijira.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *