Hukumar Hana Fasa Ƙwari ta kama haramtattun kaya na sama da Naira miliyan 362 A jihohin Adamawa da Taraba.

Hukumar  ta reshen Adamawa da Taraba ta ce ta kama haramtattun kaya da darajarsu ta haura Naira miliyan 362 cikin makonni shida da suka gabata, tare da cafke mutum biyar da ake zargi da hannun su a safarar haramtattun kayayyakin.

Jami’in hana fasa kwari Mohammed Abdullahi Tako, ya ce an samu nasarar ne sakamakon  ayyukan tattara bayanan sirri wanda  jami’an  suka gudanar a wurare daban-daban na jihohin Adamawa da Taraba.

Ya ce daga cikin manyan kayayyakin da aka kama akwai wata babbar mota kirar DAF da ke ɗauke da na’urar aikin gina hanya wadda ake zargin ana ƙoƙarin fitar da ita zuwa Jamhuriyar Chadi ba tare da bin ƙa’ida ba. An kama motar ne a ranar 9 ga watan Yuni a hanyar Gudusu–Belal da ta nufi Kamaru.

Hukumar ta kuma kama dimbin man fetur da ake zargin ana shirin fasa ƙwaurinsa zuwa ƙasashen maƙwabta. A ranar 18 ga watan Yuni an ƙwace jarkoki 370 na fetur a yankin Goshindan–Belal, yayin da a ranar 29 ga watan Yuni aka sake kama jarkoki 308 na fetur tare da fata 64 na jakuna a hanyar Mubi–Sahuda.

Haka kuma, a ranar 2 ga watan Yuli jami’an  sun kama jarkoki 181 na fetur a yankin Pariya–Wuro Bokki, sannan a ranar 15 ga watan Yuli suka ƙwace jarkoki 144 da kuma ganga mai ɗaukar lita 220 na fetur a Maiha–Wuro Alhaji.

A ranar 21 ga watan Yuli kuma, jami’an sun kama kilogiram tara na tabar wiwi a hanyar Gurin–Turrah.

A cewarsa, an kama mutum biyar da ake zargi da hannu a safarar kayayyakin, kuma ana ci gaba da bincike domin gurfanar da su a gaban kotu.

Jami’in Mohammed Tako ya ce an gudanar da dukkan ayyukan ne bisa tanade-tanaden Dokar Hukumar  ta shekarar 2023, da dokokin hana fitar da wasu kayayyaki zuwa ƙasashen waje, da kuma yarjejeniyar ƙasa da ƙasa.

Ya yi gargaɗin cewa safarar man fetur, miyagun ƙwayoyi da sassan namun daji masu kariya na barazana ga tsaron ƙasa, lafiyar al’umma da tattalin arzikin Najeriya.

Mohammmed Abdullahi Tako ya yabawa Babban Kwanturola Janar na Hukumar, Bashir Adewale Adeniyi, da sauran hukumomin tsaro, jami’an rundunar da kafafen yaɗa labarai bisa goyon bayan da suke bayarwa wajen yaƙi da fasa ƙwari.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *