Shugaban Darikar Tijjaniya na duniya, Sidi Sherif ‘Ali-Tijani, ya sauka a Najeriya, don halartar gagarumin bikin Mauludin Shehu Ahmadu Tijjani da za a gudanar a Kano.
Khalifa Sheikh Ibrahim Dahiru Bauchi, cikin rakiyar Sarkin Kano na 15, Alhaji Aminu Ado Bayero ne ya tarbi Sidi Sherif ‘Ali-Tijani a filin Jirgin Saman Nnamdi Azikiwe dake Abuja.
Da yake yi wa manema labaru jawabi Khalifa Sheikh Ibrahim Dahiru Bauchi ya ba yar da tabbacin cewa Sheikh Mahi Sheikh Ibrahim Inyass zai sauka a Abuja a Abuja a yau Alhamis da yamma don halartar wannan gagarumin biki.
- Za’a dawo fafata Gasar Carabao Cup ta Ingila
- ‘Yan Sanda sun gano maboyar ‘yan bindiga akan iyakar Filato da Bauchi
- Girgizar ƙasa a Abuja: Ministan Ma’adinai na Najeriya ya buƙaci jama’a su kwantar da hankalin su
Khalifa Sheikh Ibrahim Dahiru Bauchi ya kara da cewa, ajerin abubuwan da aka tsara gudanarwa, za a gudanar da sallar Juma’a a Masallacin Juma’a dake fadar Shugaban Kasa, a gobe Juma’a.

A cewar sa, a ranar Asabar za a gabatar da bikin saukar karatun Alqur’ani a Kano, inda za a yaye dalibai sama da 300, yayin da ranar Lahadi, za ta zamo ranar da za gudanar da gagarumin bikin Muludin a dai Kano din.
Sai ya kirayi al’umar Musulmi da su hada kawunansu, daidai lokacin da za a gudanar da babban zabe a kasar.