Asusun Kula da Kananan Yara na Majalisar Ɗinkin Duniya (UNICEF) ya ce yara fiye da biliyan ɗaya a fadin duniya suna fuskantar barazana sakamakon dumamar yanayi ta fuska uku: lafiyarsu da iliminsu da rayuwarsu.
Wani rahoton da UNICEF din ta fitar mai taken “Rahoto a kan Hatsarin da Yara Suke Fuskanta Daga Yanayi” na 2026 ya nuna cewa sauyi da ɗumamar yanayi da ayyukan ɗan Adam suka haifar suna ci gaba da sauya yanayin rayuwa a sassa daban-daban na duniya, inda yara suka kasance cikin waɗanda suka fi fuskantar illolin wannan matsala.
A cewar rahoton, matsalaolin sun haɗa da ambaliyar ruwa, da fari, da tsananin zafi, da gobara da gurgusowar hamada.
UNICEF ta ce kusan rabin yaran duniya, wato yara biliyan 1.1, suna cikin haɗarin fuskantar matsalolin na dumamar yanayi guda uku a lokaci guda.
Haka kuma, fiye da yara miliyan huɗu suna fuskantar barazanar matsaloli har guda shida da suka shafi sauyin yanayi.
- Ruto ya umarci a daina kiran jami’an tsaro masu zaman kansu da ‘masu gadi’
- Turkiyya da Saudiyya za su gana da Firaiministan Pakistan akan Gabas ta Tsakiya
- Firaiministan Pakistan Shehbaz Sharif zai kai ziyara Saudiyya
Rahoton ya ce, yara suna cikin rukunin da ɗumamar yanayi ta fi shafa saboda jikinsu wanda yaka haɓaka yana sa su fi shan wahala wajen jure matsalolin da suka haɗa da tsananin zafi, da rashin abinci, da cututtuka, da matsalolin tunani da ke biyo bayan bala’o’in muhalli.
UNICEF ta ce matsalar ɗumamar yanayi ba ta kasance abu guda kawai ba, domin yara da dama suna fuskantar haɗuwar matsaloli masu yawa a lokaci guda.
Misali, tsananin fari ka iya lalata amfanin gona tare da haifar da ƙarancin abinci.
Bushewar ciyayi sakamakon fari ka iya haddasa gobara wadda ke ƙara gurɓata iska, sannan daga baya ambaliyar ruwa ka iya lalata gidaje, da makarantu da asibitoci tare da tilasta wa iyalai yin ƙaura.
Wannan yanayi ka iya haifar da matsaloli masu dmorewa, inda lalacewar gidaje ke hana yara samun kariya daga ƙarin haɗari, yayin da katsewar karatu ke iya shafar makomarsu ta dogon lokaci tare da ƙara wahalar fita daga talauci da rashin ci gaba.
UNICEF ta yi kira ga gwamnatoci, da kamfanoni da sauran masu ruwa da tsaki da su ɗauki matakan gaggawa domin rage illolin ɗumamar yanayi da kare yara.
Ta buƙaci a rage hayakin da ke haddasa ɗumamar yanayi, a ƙara amfani da makamashin da ba ya gurabata mahalli, sannan a samar da tsare-tsaren da za su kare yara daga matsalolin muhalli.