Wani haɗarin motocin safa biyu daga wasu kamfanonin jigilar fasinjoji ya yi sanadiyyar mutuwar akalla mutane 22, ciki har da sojoji 17,da kuma raunata 37 a ranar juma’a a kudancin Jamhuriyar Nijar kamar yada ma’aikatar sufuri ta ƙasar ta bayyana.

Sashen Hausa na Rediyon Faransa Rfi ta ruwaito cewa ‘yan lokuta da aukuwar haɗarin, masu aikin ceto sun garzaya da wandada suka samu rauni zuwa asibitoci a garuruwan Madaoua da Maradi.

Haɗarin ya wakana ne a wani lokaci da hukumomi ke gudanar da gangamin wayar da kai game da haɗura a kan tituna, abin da ya zama ruwan dare a ƙasar.

A shekarar 2025, an samu rahotannin haɗurra sama da 7,000 wanda ya yi sanadiyyar mutuwar mutane sama da 1,200 da kuma raunata sama da 4,400, a cewar wani rahoto da Hukumar kula da sufuri ta Nijar ta fitar.

Hukumar dai ta alaqanta wadannan haɗɗura da gudun ganganci, tuƙi cikin maye, da kuma rashin ingancin ababen hawa da tituna.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *