Rundunar Sojin Najeriya da jami’an ’yan sandan rundunar Mobile Police Force da kuma dakarun sama na Operation FANSAN YAMMA sun fafata da wata babbar ƙungiyar ’yan bindiga a kan iyakar jihohin Zamfara da Kebbi.

Rahotanni sun ce kimanin ’yan bindiga 240 ne suka fito daga yankin Sangeko Gap a jihar Zamfara, kafin su nufi garin Makuku da ke jihar Kebbi.

Majiyoyin tsaro sun ce ’yan bindigar suna tafiya ne a kan babura, inda suka raba kansu zuwa rukuni uku yayin da suke kutsawa cikin yankin.

A yayin da dakarun ƙasa ke fafatawa da ’yan bindigar, rundunar sojin saman Operation FANSAN YAMMA ta bayar da tallafin sama domin dakile ci gaban ƙungiyar.

Lamarin ya ƙara jefa al’ummomin da ke kusa da iyakar cikin fargaba, inda rahotanni ke cewa wasu mazauna yankin sun bar gidajensu zuwa wuraren da suke ganin sun fi samun tsaro.

Jami’an tsaro na ƙoƙarin hana ’yan bindigar shiga sauran al’ummomin da ke kusa da yankin tare da dakile zirga-zirgarsu a kan iyakar Zamfara da Kebbi.

Yawan ’yan bindigar da aka ga suna tafiya tare ya sake haifar da damuwa kan tsaro a tsakanin mazauna garuruwan da ke kusa da wurin da ake gwabzawa.

Hukumomi sun shawarci mazauna yankin da su kasance cikin taka-tsantsan tare da bin umarnin jami’an tsaro yayin da aikin dakile ’yan bindigar ke ci gaba.

Mataimakin Daraktan Hulɗa da Jama’a na Rundunar Sojin Najeriya, Dibishan na 8 , Laftanar Kanar Olaniyi Osoba, ya tabbatar wa jaridar Daily Trust cewa aikin na ci gaba, inda ya ce za a fitar da ƙarin bayani bayan kammala samamen.

Lamarin na faruwa ne a yayin da rundunar soji ke ci gaba da kai hare-hare a yankin Arewa maso Yamma domin tarwatsa ƙungiyoyin ’yan bindiga, da ceto mutanen da aka sace da kuma dawo da tsaro a al’ummomin da abin ya shafa.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *