Yayin da jihar Osun ke ƙara kusantar zaɓen gwamna na ranar 15 ga Agusta, 2026, hankalin masu ruwa da tsaki ya karkata kan yadda za a tabbatar da sahihin zaɓe cikin lumana.
Hukumar Zaɓe ta Ƙasa, INEC, ta ce ta kammala shirye-shiryen gudanar da zaɓen, inda ta tabbatar da rajistar masu kaɗa ƙuri’a 2,339,233, a faɗin ƙananan hukumomi 30 da rumfunan rajista 332 da rumfunan zaɓe 3,763.
Sai dai yayin da shirye-shiryen zaɓen ke kammala, batun tsaro na ci gaba da zama muhimmin abin dubawa.
- Najeriya za ta kara da Afirka ta Kudu: Muhimman abubuwan da ya kamata ku sani
- Adeleke ya ce ba shi da kuɗin sayen ƙuri’un zaɓe
A duk wani zaɓe, rashin isasshen tsaro na iya hana wasu masu kaɗa ƙuri’a zuwa rumfunan zaɓe, tare da sanya fargaba ko tsoratar da masu zaɓe.
Saboda haka, tambayar da ke gaban hukumomin tsaro ita ce ko za a samar da isasshen tsaro a rumfunan zaɓe da sauran wuraren da ake buƙatar sa, ba tare da amfani da jami’an tsaro wajen tsoratar da masu zaɓe ko yi wa wata jam’iyya fifiko ba?
Sayen ƙuri’a
Wani babban batu da ya jawo hankalin hukumar INEC shi ne sayen ƙuri’a.
Hukumar ta nuna damuwa kan yadda wannan al’amari ke ƙara zama barazana ga sahihancin zaɓe tare da yin kira ga ‘yan jarida da su sanya ido sosai tare da fallasa duk wani yunƙurin saye ko sayar da ƙuri’a.
Wannan ya haifar da wata muhimmiyar tambayar ko idan kuɗi ya rinjayi zaɓin mai kaɗa ƙuri’a, shin za a iya cewa sakamakon zaɓen zai nuna ainihin zaɓin jama’a?
A nan ne aikin kafafen yaɗa labarai ke da muhimmanci, domin rahotannin da ake samu daga rumfunan zaɓe su kasance bisa hujja, ba jita-jita ko zargin da ba a tabbatar da shi ba.
Darasin zaɓe a Osun
Zaɓen Osun na 2022 ma ya bar muhawara kan batutuwan da suka shafi sahihancin ƙuri’u da yadda ake tantance sakamakon zaɓe.
Saboda haka, zaɓen 2026 zai kasance wani sabon gwaji ga INEC da sauran hukumomin da ke da alhakin gudanar da zaɓe cikin gaskiya.
A yanzu dai, babban abin da masu zaɓe ke jira shi ne ganin cewa an kare ƙuri’arsu da lafiyarsu da ‘yancinsu na zaɓar ɗan takarar da suke so.
Me ya kamata masu ruwa da tsaki su yi?
Jam’iyyun siyasa na da alhakin tabbatar da cewa magoya bayansu sun guji tashin hankali, yayin da hukumomin tsaro ke da alhakin kare rayuka da dukiyoyi ba tare da nuna son kai ba.
INEC kuma na fuskantar babban aiki na tabbatar da cewa kayan zaɓe sun isa inda ya kamata, jami’an zaɓe sun gudanar da aikinsu cikin gaskiya, sannan sakamakon da aka sanar ya kasance abin dogaro.
A gefe guda kuma, masu kaɗa ƙuri’a su ne ginshiƙin wannan tsari. Ƙuri’a ba ta da daraja idan aka hana mutum kaɗa ta cikin ‘yanci, ko kuma aka rinjayi zabinsa da kuɗi, ko tsoratarwa ko matsin lamba.
Zaɓen Osun na 2026 ba zai kasance gwajin ‘yan takara da jam’iyyun siyasa kawai ba. Zai kasance gwaji ne ga hukumar INEC da hukumomin tsaro da kafafen yaɗa labarai da ƙungiyoyin farar hula da kuma masu kaɗa ƙuri’a wajen kare tsarin dimokuraɗiyya.
Tambayar a nan:
Shin Osun za ta gudanar da zaɓen da zai ba kowane mai kaɗa ƙuri’a damar zaɓen cikin ‘yanci, tare da tabbatar da cewa ƙuri’ar da aka kaɗa ita ce ƙuri’ar da za ta ƙayyade wanda zai yi mulki?