Hukumar Zabe ta ƙasa INEC ta tabbatar da cewa jam’iyyun siyasa sun yi amfani da karin kwanaki uku da aka ba su domin kammala shigar da sunayen ’yan takarar su na gwamna da ’yan majalisun dokokin jihohi a zaben 2027.

Wata majiyar hukumar ta shaidawa Jaridar Daily Trust  cewa jam’iyyun sun yi amfani da karin lokacin ne bayan su da kansu suka nemi a tsawaita wa’adin, sabo da haka a fili yake cewa sun yi amfani da wannan damar.

Shugaban jam’iyyar APC na kasa, Farfesa Nentawe Yilwatda Goshwe, ya ce APC ta kammala shigar da bayanan ’yan takarar ta gabanin cikar wa’adin.

Shi ma wanda ya kafa NNPP, Dakta Boniface Aniebonam, ya bayyana cewa jam’iyyar sa ta samu damar tsayar da ’yan takara sama da kashi 90 cikin 100 na takarar da suka tsaya.

Hukumar Zaɓen ta rufe shafin da jam’iyyun ke amfani da shi wajen shigar da bayanan ’yan takara da misalin karfe 11:59 na daren Talata, 11 ga Agusta, bayan karin wa’adin kwanaki uku.

Tun da farko hukumar ta sanya ranar Asabar, 8 ga Agusta, 2026 a matsayin ranar karshe ta shigar da sunayen ’yan takarar gwamna da na majalisun dokokin jihohi.

Sai dai hukumar ta tsawaita wa’adin zuwa Talata, 11 ga Agusta, bayan da jam’iyyu su ka nemi karin lokaci.

 

Kwamishinan zabe kuma shugaban kwamitin yada labarai da wayar da kai na Hukumar zabe INEC  Mohammed Kudu Haruna, ya ce sun amince da karin lokacin ne sakamakon karuwar bukatun jam’iyyun siyasa na neman karin lokaci domin kammala aikin.

Wannan shi ne karo na biyu da hukumar zabe ta sauya wa’adin shigar da sunayen ’yan takara a shirye-shiryen zaɓe 2027, bayan wanda ta yi a cikin watan Yuli na shekarar 2026.

Ana sa ran matakin zai ba hukumar zabe damar ci gaba da sauran shirye-shiryen zaben, ciki har da wallafa bayanan ’yan takara domin amfanin jama’a.

Zaɓen gwamna da na majalisun dokokin jihohi zai gudana ne a cikin watan Fabarairun 2027.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *