Rundunar ’yan sandan jihar Osun ta gayyaci Sanata Francis Fadahunsi, mai wakiltar mazabar Osun ta Gabas, domin yi masa tambayoyi kan zargin barazanar kisa ga mambobin jam’iyyar Accord gabanin zaben gwamnan jihar da za a gudanar ranar Asabar.
An fara sukar Sanatan ne bayan wani bidiyo da ya bazu a kafafen sada zumunta, da ya nuna shi yana magana da magoya bayan jam’iyyar APC a Ilesa.
A cikin bidiyon, an ji Sanatan ya na umartar magoya bayan jam’iyyar da su kashe mambobin Accord idan suka gan su a wasu sassan Ilesa yayin gudanar da zaben.
Kalaman sun kara tayar da fargabar barkewar rikicin siyasa a jihar, yayin da ake saura kwanaki kadan a gudanar da zaben gwamna na 15 ga Agusta.
A wata wasika mai kwanan wata 11 ga Agusta, 2026, rundunar ’yan sandan ta bukaci Sanata Fadahunsi da ya bayyana halin da aka yi kalaman a cikin sa, da kuma abin da ya sa aka furta su.
Wasikar, wadda kwamishinan ’yan sanda mai kula da harkokin zabe a Jihar Osun, Samuel Etaifo Erale, ya sanya wa hannu, ta umarci Sanatan da ya bayyana a sashen binciken manyan laifuka na jihar (SCID) da ke Osogbo da karfe 11 na safe ranar Laraba, 12 ga Agusta.
A cewar wasikar, kalaman sun riga sun bazu a kafafen yada labarai da na sada zumunta.
Gayyatar ta zo ne a daidai lokacin da yanayin siyasa ke kara dumi a Osun, yayin da jam’iyyun siyasa ke kara kaimi wajen yakin neman zabe gabanin zaben gwamnan jihar na ranar Asabar.