Najeriya ta jaddada buƙatar ci gaba da zuba jari a fannin man fetur da iskar gas domin ƙara ƙarfin matatun mai da bunƙasa kasuwar makamashi a Yammacin Afirka.

An bayyana hakan ne a wajen taron karawa juna Sani na kasuwanin mai a Afrika ta Yamma, wanda Hukumar Kula da Harkokin Man Fetur ta shirya tare da haɗin gwiwar Kungiyar S & P Global da Ƙungiyar masu kula da Harkokin Makamashi ta Yammacin Afirika.

A cikin saƙon fatan alheri da ya aike wa taron, ƙaramin Ministan Albarkatun Man Fetur na Najeriya mai kula da ɓangaren mai, Sanata Heineken Lokpobiri, ya ce Najeriya ba za ta iya yin baya kan ci gaban da aka samu a ɓangaren man fetur da iskar gas ba,ya bayyana taron a matsayin wani muhimmin mataki a ƙoƙarin Afirka na samun cikakken ‘yancin kai a fannin makamashi.

Ministan ya jaddada muhimmancin ci gaba da jan hankalin masu zuba jari domin faɗaɗa ƙarfin matatun mai da bunƙasa muhimman ababen more rayuwa na man fetur da inganta hanyoyin rarraba man fetur da kuma samar da kasuwar makamashi ta yankin da za ta kasance mai gasa da juriya.

Da yake jawabi a wajen buɗe taron, Babban Daraktan Hukumar, Mallam Rabiu A. Umar, ya ce taken taron na bana ya dace da halin da kasuwar man fetur ta yankin ke ciki,ya ce taron zai ba mahalarta damar duba irin ci gaban da aka samu tun bayan taron farko da aka gudanar a shekarar 2025, tare da tattauna matsalolin da har yanzu suke akwai da kuma hanyoyin da za a bi wajen magance su.

A cewarsa, akwai buƙatar ƙara zuba jari a ababen more rayuwa da hanyoyin rarraba man fetur, tare da inganta gaskiya a kasuwa da kuma samar da yanayin da zai ba da damar kafa ingantattun farashin man fetur na yankin,ya ce yayin da taron bara ya fi mai da hankali kan kafa tubalin haɗin gwiwa, abin da ya fi muhimmanci a bana shi ne aiwatar da matakan da aka amince da su.Mallam Umar ya kuma jaddada muhimmancin Ƙungiyar Masu Kula da Harkokin Makamashi ta Yammacin Afirka wajen tabbatar da tsaron makamashi a yankin.

Ya yi kira ga hukumomin kula da harkokin makamashi da su daina takaita aikinsu ga ƙasashensu kawai, su koma ga sauƙaƙa haɗin gwiwar makamashi tsakanin ƙasashen yankin.Ya ce hakan zai haɗa da daidaita dokoki da ƙa’idoji, musayar bayanai da samar da matakan aiki iri ɗaya da kuma inganta tsarin kasuwancin makamashi tsakanin iyakokin ƙasashe.A cewarsa, irin wannan haɗin gwiwa zai taimaka wajen samar da kasuwar man fetur ta yankin da ta fi zurfi da haɗin kai.Ita ma Daraktar Zartarwa mai kula da Tsare-tsaren Tattalin Arziki da Tsare-tsaren Dabaru, Farfesa Zainab Gobir, ta ce nasarar taron ba za ta tsaya kan tattaunawar da aka yi ba.

Ta ce auna nasarar ƙungiyar zai dogara ne kan abin da za a cimma bayan kammala taron, musamman wajen ƙarfafa haɗin gwiwa, inganta sadarwa da kuma ɗaukar matakan aiwatar da abubuwan da aka amince da su.Ta buƙaci hukumomin da ke cikin ƙungiyar su fayyace nauyin da ke kansu, waɗanda za su kasance masu kula da aiwatar da ayyuka da kuma irin tallafin da ake buƙata domin mayar da shawarwarin taron zuwa ayyukan haɗin gwiwa.

Ana sa ran taron zai ci gaba har zuwa gobe, inda ake sa ran za a ci gaba da tattaunawa kan yadda za a ƙarfafa haɗin kan ƙasashen Yammacin Afirka ta fuskar tace man fetur, daidaita kasuwanni da kuma samar da tsarin tantance farashin man fetur na yankin.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *