Jam’iyyun adawa na Najeriya sun gudanar da wani babban taro ranar Asabar a birnin Badun na Jihar Oyo, inda suka fitar da sanarwar hadin gwiwa da nufin tunkarar Babban Zaben 2027.

Taron mai taken Ibadan Declaration a Turance ya samu halartar dukkanin jam’iyyun adawa, wadanda suka tattauna kan matsalolin kasa, da kuma yadda saka ce dimokuradiyya tana fuskantar barazana a karkashin mulkin jam’iyyar APC.

Daya daga cikin manyan batutuwan da suka dauki hankali a sanarwar shi ne kiran da jam’iyyun suka yi na cewa Shugaban Hukumar Zabe ta Kasa (INEC) Farfesa Joash Ojo Amupitan, ya yi murabus ko kuma kada ya gudanar da zaben 2027.

Jam’iyyun dai suna zargin Amupitan ne da nuna bangaranci ga jam’iyya mai mulki, suna cewa ‘yan Najeriya ba su da kwarin gwiwa a kansa.

Jam’iyyun adawar sun bayyana aniyarsu ta hada karfi da karfe domin fitar da dan takarar Shugaban Kasa guda daya wanda dukkaninsu za su marawa baya a zabe mai zuwa.

Wannan matakin, a cewarsu, shi ne mafita wajen ceto kasar nan daga abin da suka kira “kama-karya” da kuma yunkurin mayar da Najeriya kasa mai jam’iyya guda daya kacal.

Sun kuma jaddada cewa lallai za su shiga zabe kuma za su tsayar da nasu ‘yan takarar duk da yunkurin da suke zargin APC na yi na ganin Shugaba Bola Tinubu ne kadai zai tsaya.

Sun bukaci Majalisar Dokoki ta Kasa da ta gaggauta duba Dokar Zabe ta 2026 domin cire duk wasu sassa da ka iya shafar sahihancin zabe.

Har ila yau sun bukaci a saki dukkan manyan ‘yan siyasar da ake tsare da su ko ake muzantawa kan laifukan da za a iya bayar da belinsu.

Game da zaɓen fid da gwani kuwa, jam’iyyun sun bukaci INEC ta tsawaita wa’adin gudanar da shi har zuwa karshen watan Yuln bana, suna masu bayyana sababbin ka’idojin hukumar a matsayin “tarkon” da aka dana musu.

Ganawar tasu ta zo ne a daidai lokacin da kotu ta ajiye wasu shari’o’i da manyan jam.iyyun adawa irinsu PDP suka shigar gabanta har wani lokaci anan gaba.

Baya ga tsare Malam Nasiru El Rufa’i da ake yiwa kallon guda cikin madigan yan adawar kasar.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *