Jihar Osun na daga cikin jihohin Najeriya da aka fi samun fafatawa mai zafi a zaɓukan gwamna da suka gabata, tun bayan dawowar ƙasar nan mulkin dimokuraɗiyya a shekarar 1999.

A 1999, Adebisi Akande na AD ya lashe zaɓen, kafin Olagunsoye Oyinlola na PDP ya karɓi mulki a 2003.

A 2007, Oyinlola ya sake samun nasara a cewar sakamakon da INEC ta sanar, amma Rauf Aregbesola na ACN ya ƙalubalanci sakamakon zaɓen a kotu. Bayan shafe shekaru ana tafka shari’a, Kotun Ɗaukaka Ƙara ta ayyana Aregbesola a matsayin wanda ya lashe zaɓen a 2010.

Ra’uf Aregbesola ya sake lashe zaɓen sa a shekarar 2014, inda ya kayar da Iyiola Omisore na jam’iyyar PDP.

A 2018, fafatawar takaratsakanin Gboyega Oyetola na APC da Ademola Adeleke na PDP ta kasance cikin mafi kusa a tarihin Osun. Bayan zaɓen farko da aka bayyana a matsayin wanda bai kammala ba, an gudanar da ƙarin zaɓe, inda Oyetola ya doke Adeleke da ƙuri’u 482 kacal.

A shekarar 2022, Adeleke ya dawo inda ya kayar da Oyetola da tazarar ƙuri’u 28,344.

Sai dai kamar yadda siyasa ta gada, Oyetola ya ƙalubalanci sakamakon zaɓen a kotu, amma daga ƙarshe Kotun Ƙoli ta tabbatar da nasarar Adeleke.

Yanzu a wannan shekarar ta 2026, Adeleke na neman wa’adi na biyu, amma a ƙarƙashin Jam’iyyar Accord. APC ta tsayar da Bola Oyebamiji, yayin da Najeem Salam ke takara ƙarƙashin ADC.

Za’a gudanar da zaɓen ne a ranar 15 ga Agusta 2026, tare da sama da masu rajistar zaɓe miliyan 2.3, babban abin dubawa shi ne yawan masu kaɗa ƙuri’a da kuma ko zaɓen zai sake ɗaukar ɗumi kamar yadda aka gani a baya a shekarar 2018.

Daga Akande zuwa Adeleke, tarihin Osun ya nuna cewa siyasar jihar ta kasance mai cike da sauye-sauye, fafatawa haɗe da shari’o’in da suka taɓa sauya makomar mulki.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *