Jihar Osun da ke kudu-maso-yammacin Najeriya na da jumlar mutane miliyan 2 da dubu dari 3 da 33 da dri 2 da 33, da suka yi rajista a matsayin masu kada kuri’a, kamar yadda bayanan rajistar masu kada kuri’a da aka fitar gabanin zaben gwamnan jihar na shekarar 2026 ta nuna.
Bayanan sun nuna cewa jihar tana da kananan hukumomi 30, da kuma mazabu 332 da ake amfani da su wajen gudanar da harkokin zabe.
Haka kuma, akwai rukunin rumfunan kada kuri’a 3,763 a fadin jihar, wadanda hukumar zabe mai zaman kanta ta Najeriya, INEC, ke amfani da su wajen gudanar da zabuka.
-
Osun: Tarihin zaɓen gwamna daga 1999 zuwa 2026
-
‘Yan takarar dake kan gaba a zaben gwamnan jihar Osun
Dangane da yawan jama’a kuwa, alkaluman da aka fi amfani da su sun nuna cewa Osun na da kimanin mutane 4,705,589, bisa kiyasin da aka yi a shekarar 2016.
Sai dai wannan alkaluma na yawan jama’a tsohon kiyasi ne da aka samo daga bayanan da suka gabata, ba sabon sakamakon kidayar jama’a ba. Saboda haka, ana bukatar a bayyana shi a matsayin kiyasi idan ana amfani da shi wajen bincike ko aikin ilimi.
A takaice, jihar Osun tana da masu kada kuri’a 2,339,233, yawan jama’a da aka kiyasta a 4,705,589, kananan hukumomi 30, mazabu 332 da kuma rumfunan kada kuri’a 3,763. Alkaluman masu kada kuri’ar da sauran bayanan zabe na 2026 su ne sabbin alkaluman da suka shafi zaben gwamnan jihar da ke tafe.