Honourable James Faleke ke siya wa Tinubu tikitin tazarce akan kudi Naira miliyan 100.

Shugaban Kasa Bola Ahmed Tinubu ya shirya tsaf don neman tazarce, bayan da aka karbi takardun takararsa a hukumance.

Honorebul James Faleke, mamba a Majalisar Wakilai kuma jagoran Kungiyoyin dake Goyon Bayan Tinubu (TSG), ya karbi takardun nuna sha’awa da na takara a madadin Shugaban Kasar a kan zunzurutun kudi Naira Miliyan 100.

Wannan mataki ya zo ne mako guda bayan da Hukumar Zabe ta Kasa (INEC), a karkashin jagorancin Farfesa Joash Ojo Amupitan, ta ayyana ranar 16 ga watan Janairun 2027 a matsayin ranar Zaben Shugaban Kasa.

Sakataren Tsare-Tsare na Kasa na APC, Suleiman Argungu, ya jaddada cewa kofa a bude take ga duk wani dan jam’iyya mai sha’awa da kuma kudin takara.

Sai dai masana suna ganin cewa al’adar siyasa ta ba shugaba mai ci fifiko tana taka rawar gani, domin har yanzu babu wani jigo a APC da ya fito fili ya kalubalanci Tinubu, duk da rade-radin da ake yi cewa wasu suna sha’awa.

Yayin da jam’iyya mai mulki ke kaddamar da nata gangamin, jam’iyyun adawa na fuskantar barazana mafi girma a tarihinsu.

Baya ga jiran hukuncin shari’o’in da ke gaban Kotun Koli, akwai yunkurin Kungiyar Tsofaffin ‘Yan Majalisa da ke neman INEC ta soke wasu jam’iyyun saboda zargin take dokokin tsarin mulki.

Wannan matsin lamba na shari’a ya sanya jam’iyyun adawa cikin yanayin rashin tabbas, lamarin da ke sanya fargabar ko za a gudanar da zaben na 2027 da karfin adawa ko kuma APC za ta mamaye filin gaba daya.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *