Hadaddiyar Daular Larabawa ta fice daga kungiyar OPEC da OPEC+

A wani mataki da ka iya girgiza kasuwannin danyen mai na duniya, Hadaddiyar Daular Larabawa ta sanar da shawarar da ta yanke ta ficewa daga Kungiyar Kasashe Masu Arzikin Man Fetur (OPEC) da kawancen OPEC+, daga 1 ga watan Mayu.

A cewar wata sanarwa da Kamfanin Dillancin Labarai na kasar (WAM) ya wallafa, wannan mataki ya biyo bayan dogon nazari da UAE din ta yi ne a kan mayar da hankali kan muradun tattalin arzikin kasar na dogon lokaci, da kuma bukatar samun ‘yancin kara yawan man da take hakowa domin biyan bukatun masu zuba jari.

Sai kuma kudirin da kasar take da shi na zama jagora a sababbin hanyoyin samar da makamashi, da rage radadin dumamar yanayi, da kuma uwa uba kauce wa rikice-rikicen da Gabas ta Tsakiya ta samu kanta a ciki.

Koda yake akwai kalubale a Yankin Tekun Fasha da mashigar ruwan Hormuz, UAEn ta tabbatar wa duniya cewa za ta ci gaba da kasancewa amintacciya kuma abokiyar hulda mai fifita bukatun abokan hulda.

  “Wannan mataki ba zai sauya kudirinmu na tabbatar da daidaiton farashin mai a duniya ba.

“Sai dai zai ba mu damar amfani da karfinmu wajen samar da mai mai rahusa da kuma karancin gurbatar yanayi ga duniya cikin hanzari,” inji sanarwar.

UAE ta shiga kungiyar OPEC ne tun a shekarar 1967 ta hanyar Masarautar Abu Dhabi, kafin daga bisani ta ci gaba da zama mamba bayan kafuwar Hadaddiyar Daular a shekarar 1971, shekaru 50 da suka shude.

Masana na ganin ficewar Hadaddiyar Daular Larabawan na nufin za ta iya hako mai yadda take so ba tare da bin ka’idojin takaita hako mai da OPEC ke sanyawa kasashe ba, lamarin da ka iya zama babban kalubale ga kungiyar, musamman idan aka yi la’akari da cewa UAE ce ke kan gaba a cikin kasashe mafi karfi a kungiyar bayan Saudiyya.

Haka nan matakin ka iya jawo hankalin manyan kamfanonin mai na duniya su kara zuba jari a Abu Dhabi, ganin cewa daular tana shirin fadada ayyukanta na iskar gas da makamashin da hasken rana ke samarwa.

Babban abin jira a gani shi ne tasirin da wannan sauyi zai haifar a bangaren farashin danyen mai a kasuwannin duniya daga nan zuwa kowane lokaci.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *