Shugaban Zambiya mai ci, Hakainde Hichilema, ya samu gagarumar nasara a ƙidayar farko ta zaɓen ƙasar, lamarin da ke nuna cewa zai iya lashe zaɓen kai tsaye ba tare da zagaye na biyu ba.
Hukumar zaɓen Zambiya ta ce bayan an ƙirga kuri’u daga fiye da rabin mazabun ƙasar, Hichilema ya samu kusan kashi 59 cikin 100 na kuri’un.
Babban abokin hamayyarsa, Brian Mundubile na jam’iyyar NRPUP, yana biye da shi da kusan kashi ɗaya bisa uku na kuri’un.
A tsarin zaɓen shugaban ƙasar Zambiya, ɗan takara na bukatar samun sama da rabin kuri’un da aka kada domin samun nasara kai tsaye, kuma ana sa ran hukumar zaɓen za ta kammala sanar da sakamakon cikin ‘yan kwanaki masu zuwa.
-
FLA ta saki sojojin Mali da suke fama da raunuka
-
WAFCON 2026: Aljeriya ta lashe tagulla bayan ta casa Marokko
Sai dai ana gudanar da zaɓen ne cikin yanayi mai cike da zarge-zargen tsoratarwa da tashin hankali. Masu sa ido na ƙasa da ƙasa sun ce yaƙin neman zaɓen ya kasance ba daidai ba, tare da nuna fifiko ga shugaban da ke kan mulki.
An dakatar da tattara sakamakon zaɓen na kusan sa’o’i shida a ranar Juma’a bayan rahotannin tashin hankali kan ma’aikatan zaɓe da kuma zargin satar kuri’un da aka riga aka yi wa alama.
Tawagar masu sa ido ta Tarayyar Turai ta ce dakatarwar ta yi tsauri, saboda ƙananan cibiyoyin zaɓe ne kawai abin ya shafa.
Hukumar zaɓen ƙasar ta ce yanzu an shawo kan barazanar da ta kawo cikas ga ƙidayar kuri’un. Sai dai wani jami’in zaɓe mai shekara 57 ya mutu a kusa da Lusaka, babban birnin ƙasar a ranar zaɓe, inda ‘yan sanda suka kama mutane tara bisa zargin hannu a lamarin.
Jam’iyyar NRPUP ta kuma yi wani zargi mai tsanani cewa wasu jami’an tsaro dauke da makamai, waɗanda take ganin sojojin Zambiya ne, sun shiga gidan Brian Mundubile da ke Lusaka a daren Juma’a, inda ta ce wani ɗan majalisa ya samu rauni sakamakon harbin bindiga, yayin da aka tafi da wasu mutane ba tare da sanin inda aka kai su ba.
Sai dai Mundubile ya ce babu wata magana ta siyasa da za ta iya sauya ma’anar abin da ya faru, amma ya yi kira ga magoya bayansa da kada su ɗauki matakin ramuwar gayya. Zuwa lokacin da rahoton ya fito, hukumomin Zambiya ba su mayar da martani kan wannan zargi ba.
Tawagar sa ido ta Tarayyar Turai ta bayyana ganin wani mutum da aka kama da karfin tsiya, yayin da jami’an tsaro ke dauke da makamai a safiyar 10 ga Agusta.
A rahoton tawagar na farko, ta bayyana zaɓen a matsayin mai cike da adawa da cewa ya karkata zuwa ga Hichilema, musamman yadda kafafen yaɗa labarai na gwamnati suka fi nuna goyon bayan su gare shi.
Zambiya ta kasance ƙasar dake samun sauyin mulki cikin lumana ta hanyar gudanar da zaɓe tun bayan komawar ta tsarin jam’iyyu da dama a shekarar 1991.
Hichilema ya samu gagarumar nasara a zaɓen 2021, kuma wa’adin sa na farko ya zo da bunƙasar tattalin arziki, duk da dimbin arzikin tagulla da sauran ma’adanai da ƙasar ke dashi, bankin duniya ya kiyasta cewa sama da kaso 70 cikin 100 na ‘yan kasar miliyan 22 na rayuwa ne kasa da dala Uku a rana.