Hukumar Yaki da Cin Hanci da Rashawa ta Najeriya (EFCC) reshen Kano ta fara binciken wani mutum mai suna Haruna Yusuf, wanda Jami’an Kwastam suka kama shi da wasu kuɗaɗen ƙasashen waje a filin jirgin sama na Mallam Aminu Kano.

Kuɗaɗen da aka kama sun haɗa da dala $73,000, fam £15,957 da kuma Riyal na Saudiyya 827,800.

An fara binciken ne bayan Mukaddashin Kwanturolan Kwastam na shiyyar Kano/Jigawa, DCU Adamu, ya miƙa wanda ake zargin da kuɗaɗen ga EFCC a Kano.

An gano kuɗaɗen ne yayin aikin binciken fasinjojin da suka shigo ƙasar tsakanin 8 zuwa 12 ga Agusta, 2026. Kuɗaɗen sun haura adadin da doka ta amince mutum ya shigo da su ba tare da bayyana wa hukumomi ba.

Mukaddashin Daraktan EFCC na shiyyar Kano, AC S. Ebelo, ne ya karɓi wanda ake zargin da kuɗaɗen a madadin hukumar.

A ranar 8 ga Agusta, 2026, da misalin ƙarfe 2:20 na rana, jami’an Kwastam da ke gudanar da binciken fasinjoji a bangaren ɗaukar kaya sun gano wani akwati na Saudi Air,  cikin akwatin an gano Riyal na Saudiyya 827,800 da dala $53,300, waɗanda aka ɓoye a cikin takalmi.

Haka kuma, a ranar 12 ga Agusta, 2026, da misalin ƙarfe 1:50 na rana, jami’an Kwastam sun dakatar da wani akwati mallakin Haruna Yusuf, a jirgin Ethiopian Airlines mai lamba ET941.

A yayin binciken na biyu ta amfani da fasahar Non-Intrusive Inspection, an gano dala $20,000 da fam £15,957 waɗanda aka ɓoye a cikin takalman wasanni.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *