Ministan Labarai da Wayar da Kan Jama’a, Mohammed Idris, ya ce babban ƙalubalen da ke gaban tsarin ilimin manyan makarantu a Najeriya a yanzu ba wai ƙara gina gine-ginen makarantu kaɗai ba ne, illa tabbatar da cewa ilimin da ake bayarwa a cikin waɗannan gine-ginen yana da inganci kuma yana samar da amfanin da zai amfani al’umma.

Ministan ya bayyana hakan ne a Lokoja, babban birnin Jihar Kogi, yayin wani taron tattaunawa da masu ruwa da tsaki kan ilimi na shiyyar Arewa ta Tsakiya, wanda Asusun Tallafawa Manyan Makarantu, TETFund, ya shirya.

Mohammed Idris ya ce duk da cewa gwamnati na kashe biliyoyin naira wajen tallafawa manyan makarantu ta hanyar TETFund, ya zama wajibi irin waɗannan kuɗaɗe su samar da sakamako na zahiri, musamman wajen inganta ƙwarewar ɗalibai da kuma taimaka wa ci gaban tattalin arzikin ƙasa.

Ya ce bai kamata a duba nasarar tsarin ilimi ta fuskar yawan gine-ginen da aka samar kaɗai ba, sai dai a tambayi irin ilimin da ɗalibai ke samu da kuma ko suna fita daga makarantu da ƙwarewar da za ta ba su damar samar da ayyukan yi da warware matsalolin da ke addabar al’umma.

Ministan ya kuma ce shiyyar Arewa ta Tsakiya, na da dimbin albarkatun noma, ma’adanai da makamashi, saboda haka jami’o’i da kwalejojin yankin ya kamata su zama cibiyoyin bincike da kirkire-kirkire domin bunƙasa waɗannan albarkatu, maimakon samar da ɗalibai da burinsu kawai ya ta’allaka kan samun aikin gwamnati.

Mohammed Idris ya kuma danganta ingantaccen ilimi da samar da tsaro da zaman lafiya a ƙasa. A cewarsa, matashin da ya samu ingantaccen ilimi tare da ƙwarewar sana’a da damar amfani da basirarsa wajen samun abin dogaro da kai, zai fi samun kariya daga shiga aikata laifuka, bangaranci da tsattsauran ra’ayi.

Ministan ya kuma yi kira ga cibiyoyin ilimi da su gaggauta sabunta tsarin koyarwarsu domin tafiya da sauye-sauyen da ake samu a duniya, musamman sakamakon bunƙasar fasahar Artificial Intelligence, wato AI, da kuma amfani da na’urorin zamani wajen gudanar da ayyuka.

Ya ce akwai buƙatar a shirya ɗaliban Najeriya domin su samu ƙwarewar da za ta ba su damar taka muhimmiyar rawa a sabuwar kasuwar ayyukan yi, maimakon su zama waɗanda sauye-sauyen fasaha za su maye gurbinsu.

Mohammed Idris ya kuma jaddada ƙudirin gwamnatin Shugaba Bola Ahmed Tinubu na faɗaɗa damar samun ilimi ta hanyar Asusun Lamunin Dalibai, NELFUND, domin taimaka wa ɗaliban da ke fuskantar matsalar kuɗi su ci gaba da karatunsu.

A ƙarshe, Ministan ya buƙaci TETFund da shugabannin manyan makarantu su tabbatar da gaskiya, amana da kyakkyawan amfani da kuɗaɗen da ake warewa fannin ilimi, yana mai cewa duk wani kuɗin da aka kashe a harkar ilimi ya kamata ya haifar da amfani na zahiri ga ɗalibai da al’ummar Najeriya.

By Bashar Muhammad Dange

Bashar Muhammad is a Nigerian multimedia journalist, broadcaster, producer, and media professional with years of experience in radio broadcasting, reporting, and content creation. He holds a B.Sc. in Mass Communication from Ahmadu Bello University, Zaria, and a Diploma in Mass Communication from The Polytechnic of Sokoto. Throughout his career, Bashar has produced and presented programmes on current affairs, agriculture, health, education, and community development. He has worked with leading media organizations including Garkuwa FM 95.5 Sokoto, Trimming Radio 96.5 FM Goronyo, Giantability Media Network, and ABU Samaru FM. As a journalist and presenter, he has conducted interviews, reported on social and developmental issues, and amplified the voices of underserved communities. Beyond broadcasting, Bashar has demonstrated leadership in media management, programme development, and team coordination. He has received several awards and recognitions for his contributions to journalism, Hausa language development, and community service. His expertise includes radio production, news reporting, sound editing, investigative journalism, media analysis, and public presentation. Driven by a passion for impactful storytelling and public service, Bashar Muhammad continues to use journalism and media platforms to inform, educate, and empower communities across Nigeria.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *