Bayan da Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta Kasa ta sanar da ɗage takunkumin yaƙin neman zaɓen 2027 ga masu takarar shugabancin ƙasa da Majalisar Dokoki ta Ƙasa, fitattu daga cikin ‘yan takarar shugabacin Najeriya sun fara fitowa fili don bayyana manufofin su ga masu zaɓe.
A yayin ɗan takarar Shugabancin Ƙasa na jam’iyyar ADC, Atiku Abubakar ya ayyana ƙudirin sa na dawo da tallafin mai, Shugaba Tinubu, na jam’iyyar APC mai mulki, baje kolin nasarorin da gwamnatinsa ta cimma ya yi, a matsayin matakin farko na tallata kan sa ga al’umar Najeriya.
- Hukumar tsaro ta DSS ta saki mutumin da ake zargin ɗan Boko Haram ne
- Abacha: A daina yaɗa ƙarya kan matattu, Al-Mustapha ga tsohon jami’in DSS
- Hukumar tsaron farin kaya ta DSS ta rufe shari’arta kan Nasir El-Rufa’i
A matsayin mataki na farko na tallata manufofi da shirye-shiryensa na tallata kan sa ga ‘yan Najeriya, bayan janye takunkumin yakin neman zabe da hukumar zabe mai zaman kanta ta yi, Shugaba Bola Tinubu ya umarci ministan kudi, Taiwo Oyedele da ya yi wa ‘yan Najeriya bayanin irin nasarorin da gwamnatinsa ta samu tun bayan da aka rantsar da ita izuwa yanzu da kuma bayanin saura ayyukan da suka ke gaban ta.
Tinubu ya ce shawarwari masu wuya da gwamnatinsa ta rufe ido ta yanke, a yau sun haifar da da mai ido, yana mai karawa da cewa, ‘yan Najeriya sun cancanci sanin sauye-sauyen da aka samu.
Ya ce ‘wannan gwamnatinku ce, kasarku ce kuma wannan shi ne abinda mu ka gudanar domin ku’.
Shi kuwa Atiku Abubakar, dawo da tallafin man fetur shi ne babban abin da, ya zuwa yanzu ya fito fili ya ce idan an zabe shi zai yi.
A wata hira da ya yi da manema labaru ta kafar facebook, Atikun ya ce zai dawo da tallafin man fetur, abin da ya ce zai cire yayin yakin neman zaben sa a 2023.
Ya nuna cewa bayan cire tallafin man, ‘yan Najeriya ba su gani akasa ba, duk da dimbin kudaden da gwamnatin tarayya ta tara daga hakan, yana mai shan alwashin gurfanar da duk wadanda suka ci kudaden da aka samu daga cire tallafin mai a kasar.
Daga Ofishin yaɗa labarai na ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar NDC, Peter Obi, Kakakinsa Idris Zekeri ya buƙaci ‘yan Najeriya da su auna dukkan ‘yan takarar shugaban ƙasa bisa la’akari da tarihin aikinsu da ra’ayoyinsu da kwarewa da kuma halayensu.
Ofishin yaɗa labaran ya bayyana cewa yaƙin neman zaɓen Obi zai mayar da hankali ne ga sauya Najeriya daga ƙasa mai sayowa zuwa ƙasa mai samarwa da rage tsadar gudanar da gwamnati da inganta ilimi da kiwon lafiya, da tsaro, da kuma samar da damammaki ga matasan Najeriya.
A yayin da shugaba Bola Tinubu ke tinkaho da nasarorin da gwamnatin sa ta cimma wajen tallata kan sa ga ‘yan Najeriya, su kuwa Atiku Abubakar da Peter Obi dogaro su ke yi da abin da suke ganin gazawa ce ta gwamnati don neman kuri’un ‘yan Najeria a Zaben Shugaba Kasa da za a gudanar a 2027.