Sojojin hadin gwiwa na shiyyar Arewa maso Yamma masu gudanar da aikin Operation FANSAN YAMMA (JTF NW OPFY) sun ci gaba da kai hare-hare a yankunan da suke gudanar da ayyukansu, inda suka ceto wani mutum da aka yi garkuwa da shi a Jihar Kaduna, sune kuma suka dakile harin ’yan ta’adda a Jihar Sokoto.

A ranar 20 ga watan Agusta, 2026, sojojin Sashe na 1 sun amsa kiran gaggawa bayan sace wani mutum mai shekaru 43 a kewayen yankin Awon da ke Karamar Hukumar Kachia a Jihar Kaduna.

Cikin hanzari sojojin suka isa yankin inda suka bi sahun ’yan ta’addar har cikin kurame, lamarin da ya tilasta wa ’yan ta’addar barin mutumin da suka yi garkuwa da shi sannan suka tsere.

Daga baya an mayar da mutumin da aka ceton zuwa ga iyalansa.

A wani samame na daban a ranar 21 ga watan Agusta, 2026, sojojin Sashe na 2, tare da hadin gwiwar jami’an tsaro na sa-kai na yankin, sun fatattaki ’yan ta’adda da suka kai hari a Kauyen Kwaren Gamba da ke Karamar Hukumar Sabon Birni a Jihar Sokoto.

Jami’an tsaron sun yi fito-na-fito da ’yan ta’addar, lamarin da ya tilasta musu tserewa a guje cikin rudani.

Yayin da suke bin sawun ’yan ta’addan da ke tserewa, an kashe dan ta’adda guda daya, sannan sojojin sun gano wayoyin salula guda 2 da tsabar kudi da katin cire kudi na ATM da katunan lodi na waya, da sauran wasu kayayyaki a wurin da abin ya faru. 

Rukunin dakarun hadin gwiwa na Arewa maso Yamma na Operation FANSAN YAMMA sun ce sun kuduri aniyar dorewa da kaimi wajen gudanar da ayyukansu na yanzu don hana ’yan ta’adda gudanar da ayyukansu cikin walwala, sannan da samar da ingantaccen tsaro ga al’ummomin da ke cikin yankunan gudanar da ayyukan sojin.

Hedikwatar rundunar ta sake tabbatar wa jama’a cewa dakarun za su ci gaba da mayar da martani cikin gaggawa ga duk wata barazana da ta taso, yayin da take kira ga ’yan kasa da su ci gaba da kasancewa cikin shirin ko-ta-kwana, sannan su rika bayar da bayanai masu inganci akan lokaci ga jami’an tsaro domin tallafa wa kokarin da ake yi na maido da zaman lafiya da tsaro mai dorewa.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *