Hull City ta fara kakar gasar Premier League ta 2026/27 da gagarumar nasara, bayan ta doke Manchester United da ci 2–0 a wasan da suka fafata.
Hull City ta nuna ƙarfi tun farkon wasan, inda ta yi amfani da ƙwallayen da aka samo daga kai hare-hare ta gefen fili da kuma bugun tazara, abin da ya jefa Manchester United cikin matsala.
Semi Ajayi da Nobel Mendy ne suka zura ƙwallayen biyu da suka bai wa Hull City damar tafiya hutun rabin lokaci tana kan gaba da ci 2–0.
- Arsenal ta lallasa Coventry a wasan bude kakar Firimiyar Ingila na bana
- Julián Álvarez ya shirya kakar wasa ta uku a Atlético Madrid
- Cristiano Ronaldo ya fara kakar wasan bana da ƙafar dama
Bayan dawowa hutun rabin lokaci, Manchester United ta yi ƙoƙarin farfaɗowa, inda ‘yan wasanta suka ƙara matsa lamba tare da ƙoƙarin samar da damammaki a gaban ragar Hull City.
Sai dai yan wasan Hull sun ci gaba da kasancewa cikin tsari, inda suka hana United samun damar da za ta iya sauya sakamakon wasan.
Kocin Manchester United, Michael Carrick, ya yi wasu sauye-sauye ciki har da shigar da Kobbie Mainoo da Benjamin Šeško, amma sauye-sauyen ba su haifar da canjin da ake bukata ba.
Hull City kuwa ta ci gaba da nuna ƙwazo wajen kare ragarta da kuma dakile hare-haren United har zuwa ƙarshen wasa.
Daga bisani aka tashi wasan Hull City 2, Manchester United 0.
Wannan nasara ta kasance ta musamman ga Hull City, domin ita ce nasararta ta farko a kan Manchester United a gasar lig cikin shekaru 52.
Magoya bayan Hull City sun yi shagali bayan wasan, inda suka nuna farin ciki da yadda ƙungiyarsu ta fara kakar bana da babbar nasara.
A gefe guda, sakamakon ya kasance mummunan farawa ga Manchester United, wadda za ta nemi gyara kura-kurenta a wasannin da ke tafe.