Tsohon Gwamnan Jihar Rivers, Rotimi Amaechi, ya yi kira da a ƙara saka jari wajen inganta jin daɗin tattalin arziki da lafiyar mata, yana mai cewa ba za a iya raba lafiyar mata da ƙarfin tattalin arzikin ƙasa ba.

Amaechi ya bayyana hakan ne a ranar Juma’a a Abuja, yayin taron Her Health, Her Power Conference Africa 2026, wanda Gidauniyar Vicky Heldan ta shirya.

Ya ce mata, musamman waɗanda ke aikin noma, suna buƙatar samun ingantattun damar tattalin arziki da kuma kulawar lafiya domin su samu damar bayar da gudummawa mai ma’ana ga ci gaban ƙasa.

“Ba za ka iya sa mace ta kasance cikin koshin lafiya da ƙarfi ba idan tattalin arzikin ƙasar yana cikin mummunan hali,” in ji Amaechi.

Ya bayyana cewa tsakanin kashi 40 zuwa 60 cikin 100 na matan Najeriya suna aikin noma, yana mai jaddada buƙatar samar da manufofin da za su inganta damar mata na samun hanyoyin dogaro da kai da kuma kiwon lafiya.

Amaechi ya ce shugabannin siyasa suna da alhakin samar da yanayin da zai ba mata damar rayuwa cikin ƙoshin lafiya da kuma samar da abin da zai ba su damar bada tasu gudunmuwar wajen ci gaban ƙasa.

Ya kuma yi kira da a ƙara saka jari a fannin ilimin mata, yana cewa mata masu ilimi suna da kyakkyawar damar zama shugabanni nagari.

Da yake waiwayen zamaninsa a matsayin Gwamnan Rivers, Amaechi ya ce gwamnatinsa ta kafa cibiyoyin lafiya a sassa daban-daban wa wajen rage mace-macen mata masu juna biyu da yara.

Ya ce an ɗauki likitoci da ma’aikatan jinya aiki a cibiyoyin, sannan aka bai wa mata masu juna biyu tallafin kuɗi domin ƙarfafa musu gwiwar zuwa asibiti domin duba lafiyar ciki kafin haihuwa.

A cewarsa, wannan mataki ya taimaka wajen magance matsalolin kiwon lafiya da kuma na tattalin arziki da mata ke fuskanta.

“Dole ne a mayar da iyayenmu mata ƙauyuka domin tabbatar da cewa an sauya ƙauyukan zuwa wuraren da za a iya rayuwa cikin walwala, a gina asibitoci da cibiyoyin lafiya, sannan a ɗauki likitoci aiki domin kula da matsalolin lafiyar mata,” in ji shi.

Amaechi ya kuma bukaci masu ruwa da tsaki su fahimci alaƙar da ke tsakanin jin daɗin mata da kuma lafiyar al’umma baki ɗaya.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *