Tawagar Ƙwallon kwando ta mata ta Najeriya, D’Tigress, ta sha kaye mai zafi da ci 83-58 a hannun Spaniya a wasan shirye-shiryen tunkarar Gasar Cin Ƙwallon Kwando ta Mata ta Duniya ta 2026 da za a ayi a kasar Jamus.
D’Tigress ta fara da karfi a rabi na farko, inda ta mamaye wasan kuma ta hana tawagar Spaniya yin kataɓus.
-
NPFL Super 6: Rangers za ta kara da Plateau United a wasan ƙarshe
-
Mourinho ya fara kakar wasa da kafar dama
-
Dalilin da ya sa MLS ta ci tarar Lionel Messi
Amma da aka dawo daga hutun rabin lokaci, Spaniya ta dawo da ƙarfinta, yayin da ta mamaye wasan rabi na biyu gaba daya, inda ta rika samun maki akan Najeriya.
Kusan dukkan hare-haren da ‘yan wasan Spaniya suka kai ya shiga raga, yayin da Najeriya ta kasa canza akalar wasan. Victoria Macaulay ce kan gaba wajen ci wa D’Tigress ƙwallaye da maki 18, amma ƙoƙarin ta kadai bai isa ya hana Najeriya shan kaye ba.
A Yanzu, D’Tigress za ta yi kokarin tsayawa da kafafunta lokacin da za ta kara da Belgium a wasansu na gaba.