Kungiyar kare haqqin bil’adama (SERAP) ta bukaci Shugaban Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Kasa (INEC), Farfesa Joash Amupitan da ya gaggauta bayyana ko hukumar ta yi amfani da ikon da doka ta ba ta na sanya iyaka kan gudummawar da ake bayarwa ga harkokin siyasa, kamar yadda sashe na 91 na Dokar Zabe ta 2026 ya tanada.

SERAP ta ce idan INEC ta sanya irin wadannan iyakoki, ya kamata ta wallafa su tare da sanar da jam’iyyun siyasa, ‘yan takara, masu bayar da gudummawa da kuma jama’ar Najeriya gaba daya.

Kungiyar ta kuma bukaci INEC ta bayyana tsare-tsare, ma’aikata da hanyoyin da ta tanada domin sa ido, gudanar da bincike da tabbatar da bin dokokin da suka shafi gudummawar siyasa da kuma kudaden yakin neman zabe a yayin shirye-shiryen zaben 2027.

SERAP ta kuma bukaci hukumar ta bayyana yadda take sa ido kan harkokin kudaden siyasa, ciki har da hanyoyin ganowa da magance gudummawar kudi kai tsaye da ta hanyar kayayyaki ko ayyuka, kudaden da ake bi ta kafafen zamani da shafukan sada zumunta, , da gudummawar da ake bayarwa ta hannun wasu mutane domin kaucewa iyakokin da doka ta sanya.

A cikin wata bukatar samun bayanai karkashin Dokar ‘Yancin Samun Bayanai (Freedom of Information) mai kwanan wata 22 ga Agusta 2026, wadda Mataimakin Daraktan SERAP, Kolawole Oluwadare, ya sanya wa hannu, kungiyar ta ce:

“Kara bayyana gaskiya a harkokin kudaden siyasa na da matukar muhimmanci domin tabbatar da cewa an gudanar da zaben 2027 cikin daidaito, tare da bai wa ‘yan kasa damar yin zabin siyasa cikin ‘yanci da cikakken sani.”

SERAP ta ce aikin INEC na tsarin mulki ba wai karbar bayanan kudaden jam’iyyun siyasa kawai ba ne. A cewarta, Kundin Tsarin Mulkin Najeriya ya bukaci hukumar ta binciki harkokin kudaden jam’iyyun siyasa, ta gudanar da binciken da ya dace sannan ta gabatar da rahotonta ga Majalisar Dokoki ta Kasa.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *