Rundunar ‘Yan sanda a jihar Kaduna, ta ceto mutane 76 da wasu ‘yan bindiga suka yi garkuwa da su a ƙaramar hukumar Birnin Gwari.

Rahotanni sun ce waɗanda aka yi garkuwa da su,  sun haɗa da maza, mata da ƙananan yara, lamarin ya faru ne lokacin suna cikin motocin haya,  inda ‘yan bindigar suka tare su a kauyen Folwaya, kusa da Birnin Gwari.

Lamarin ya faru ne a ranar 19 ga watan Agustan 2026 da misalin karfe 5:30 na yamma, Rundunar ‘yan sandan ta ce ta samu bayanan sirri daga reshen kungiyar ma’aikatan sufuri ta ƙasa, NURTW, da ke Birnin Gwari.

Bayan sace mutanen, ‘yan bindigar sun kai su cikin wani daji tare da ɓoye su a cikin wani kogo da ke wani yanki mai tsaunuka. Hakan ya sa rundunar ‘yan sanda ta gaggauta tura wata tawaga ta musamman daga ofishin ta dake Birnin Gwari.

Jami’an ‘yan sandan sun kai farmaki yankin, lamarin da ya tilasta wa ‘yan bindigar tserewa tare da barin mutanen da suka yi garkuwa da su. Daga bisani jami’an sun samu nasarar kuɓutar da dukkan mutane 76 ba tare da samun wani rauni ba.

Kwamishinan ‘yan sandan jihar Kaduna, CP Rabiu Muhammad, ya yaba wa kungiyar ma’aikatan sufuri ta ƙasa NURTW reshen Birnin Gwari, bisa bayar da bayanai da suka taimaka mata wajen gudanar da aikin ta.

Kwamishinan ya buƙaci jama’a da su ci gaba da taka-tsantsan tare da kai rahoton duk wani mutum ko motsi da ake zargi ga ‘yan sanda cikin gaggawa.

Ya kuma gargadi jama’a da kada su ɗauki doka a hannun su, yana mai cewa hakan na iya jefa rayukan mutane marasa laifi cikin hadari.

 

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *