Rundunar ’yan sandan jihar Kaduna ta ce ta ceto mutane uku da ake zargin ’yan bindiga sun yi garkuwa da su a karamar hukumar Makarfi ta jihar.
Rundunar ta ce ta samu sahihin bayanan sirri a ranar 21 ga watan Agustan 2026 kan wasu mutane da ake zargin ’yan bindiga ne da ke gudanar da harkokinsu a kusa da Gidan Mijin Gwaggo da ke yankin Durum, a karamar hukumar Makarfi.
Bayan samun bayanan, kwamishinan ’yan sandan jihar Kaduna, Rabiu Muhammad, ya umarci jami’an sashen ’yan sandan Makarfi da su jagoranci sintiri tare da hadin gwiwar ’yan banga zuwa yankin, rundunar ta ce da ’yan bindigar suka ga jami’an tsaro, sai suka bude musu wuta.
An ce jami’an sun mayar da martani, inda aka dauki tsawon lokaci ana musayar wuta, daga bisani, ’yan bindigar suka tsere zuwa cikin daji dauke da raunukan harbin bindiga.
A yayin bincike, jami’an tsaron sun gano wani gida mallakar wani mutum mai suna Yakubu Sule, da ake amfani da shi a matsayin maboyar ’yan bindiga, inda anan ne kuma aka gano wasu mutane uku da ake zargin an yi garkuwa da su.
Daga cikin wadanda aka ceto akwai Alhaji Hamza Shuaibu Gimi da wasu mutum biyu, wanda rundunar ta ce an ceto su ba tare da wata matsala ba, sannan an kuma kwato babur kirar Boxer da ake zargin masu garkuwar sun yi amfani da shi.
Daga bisani an mayar da mutanen ga iyalansu, yayin da jami’an tsaro ke ci gaba da kokarin cafke wadanda suka tsere.
Kwamishinan ’yan sandan Kaduna ya yabawa jami’an tsaron da kuma ’yan bangar da suka shiga aikin, tare da kira ga jama’a da su ci gaba da bai wa jami’an tsaron sahihan bayanai domin dakile ayyukan masu laifi.