Sufeta Janar na ‘Yan Sandan Najeriya, Tunji Disu, ya baiwa kwamishinonin ‘yan sandan kasar  umarnin gurfanar da waɗanda aka kama da laifukan kisan kai ta hanyar daukar doka a hannu kan laifukan da ake tuhumar su da aikatawa na kisan kai da gangan.

Cikin wani faifan bidiyo da rundunar ta wallafa a shafin ta na X, Disu ya umarci Kwamishinonin ‘Yan Sandan jihohi kasar da Birnin Tarayya Abuja cewa daga yanzu su rika daukar batun a matsayin kisan kai da gangan.

Disu, ya bayyana cewa babu wata al’umma, ko kuma kowacce irin kungiyar ta tsaro a Najeriya da ke da ikon kamawa, ko gabatarwa gaban shari’a, ko yanke hukunci, ta hanyar kisa, bisa kowane irin zargi ko jita-jita, ko kuma wata shaidar da aka gani a kafafen sada zumunta.

“Daukar doka a hannu babban Laifi ne da rundunar ‘Yan Sandan Najeriya za ta bi hakki akai, domin babu wani dan kasa, al’umma, ko kungiya da ke da hakkin yi wa wani shari’a ballantana yanke masa hukunci ko kuma kashe shi,” in ji Disu.

Sufetan yace bisa l’akari da Sashe na 33, 34, da 36 na tsarin mulkin Najeriya na shekarar 1999, sassan dokar sun tabbatar wa kowane dan Najeriya har da wanda ake zargi hakkin rayuwa, kare mutunci, da tabbatar da dalaci yayin da yake gaban shari’a.

Haka nan “Sashe na 319 na kundin manyan laifuka da na 221 na Kundin hukunta laifukan sun bayyana wannan a fili cewa, duk mutumin da ya kashe wani ba tare da bin doka ba, laifin kisa da gangan ya hau kansa, ko da kuwa ba da gangan yayi kisan ba.

Sannan Sufetan ya kara da cewa duk wanda ya tsara, ko tunzura, ko ma karfafa gwiwar fusatattun mutane ta hanyar ba su goyon baya, koda bai sa hannun sa jikin wanda aka kai wa harin ba alhakin aikatawar yana wuyan sa.

Haka nan, wadanda suka yada bidiyon yadda akayi kisan, ko suka goyi bayan hakan, za a tuhume su da laifin haɗin baki, kuma zasu iya kaiwa ga girbar hukuncin daurin shekaru 14 a gidan yari.

Disu ya faɗi labarin kisan mutane 16 da aka yi a Uromi, Jihar Edo a watan Maris na shekarar 2025, a matsayin tunatarwa kan sakamakon daukar doka a hannu.

Ya ce makamantan wadannan abubuwa sun haifar da kashe mutane sakamakon zarge-zargen da basu da tushe, ciki har da daliban da aka zarga da satar wayoyi, da matafiyan da aka yi kuskuren daukar su a matsayin bata-gari, da kuma matasan da aka kai wa hari kan zargin batanci ko asiri.

Sufetan yace ya baiwa kwamishinonin ‘yan sandan Najeriya da Abuja umarnin daga yanzu, su rika daukar lamarin kisan kai da fusatattun mutane ke yi a matsayin na ganganci, kuma su tabbatar da gabatar da sigar hakan a cikin takardun shigar da kara.

Ya bayyana cewa masu bincike za su dogara ne kan na’urorin daukar bidiyo, shaidar gani da ido, bayanan sirri na al’umma, da shaidun bincike da na kwarewar kimiyya domin gano wadanda suka aikata laifin.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *