Sarki Oyo Nyimba Kabamba Iguru Rukidi na hudu, da ya kafa tarihin kasancewa sarki mafi karancin shekaru a duniya bayan ya haye karagar mulki yana dan shekara uku kacal a Uganda.
Ya rasu, bayan fama da rashin lafiya.
Firayim Ministan Masarautar Tooro, Calvin Armstrong Rwomiire Akiiki, shine ya sanar da labarin mutuwar basaraken a ranar Juma’a, inda ya bayyana cewa sarkin ya rasu ne a ranar Alhamis, yana da shekaru 34.
Duk da ba a bayyana takamaiman cutar da ta yi sanadiyyar mutuwar ta sa ba, kafafen yada labarai na cikin gida a Uganda sun jiyo wani ministan gwamnati yana cewa sarkin ya shafe wani lokaci yana jinya a kasar Amurka kafin rasuwar tasa.
Yayin da yake sanar da wannan mummunan labari, Firayim Minista Akiiki ya bayyana rasuwar sarkin a matsayin wata babbar asara da ba za a iya mai gurbinta ba ga daukacin kasar Uganda, da kuma al’ummar masarautar Tooro.
“Ina kiran dukkan al’ummar masarautar Tooro da su kasance masu hadin kai da kwanciyar hankali da kuma addu’a a wannan lokaci na alhini da jarrabawa, Allah ya jikansa da rahama.” Inji Firayminista Rwomiire Akiiki
Gadon Sarauta da yarinta
Sarki Oyo ya gaji karagar mulki ne a shekarar 1995 bayan rasuwar mahaifinsa, Sarki Patrick Matthew Kaboyo Rukidi na uku, sakamakon karancin shekarun sa a wancan lokacin, an nada wasu gogaggun mutane da suka hada da mahaifiyarsa domin yi masa rikon kwarya har zuwa lokacin da ya balaga.
Wannan yanayi ya sanya littafin tarihin manyan batutuwa na Guinness World Records yi masa rijista a matsayin sarki mafi karancin shekaru a duniya.
An gudanar da bukukuwan nadin sarautar sa na karshe ne a shekarar 2010 lokacin da ya cika shekaru 18 a duniya.
Sarki Oyo shine sarki na 13 a daular Tooro da aka kafa tun farkon karni na 19.
A tsawon shekaru 31 da ya shafe a kan karagar mulki, sarki Oyo ya zama madubin dubawa ga matasa a kasar Uganda, wajen gina matasa da bunkasa ilimi da tattalin muhalli da kuma yakin yaki da cuta mai karya garkuwar jiki HIV/AIDS.
Batun gadon Masarautar Tooro
Duk da cewa Sarki Oyo, bai yi aure a hukumance ko al’adance kafin rasuwarsa ba, masarautar Tooro ta tabbatar wa al’umma cewa babu matsala wajen samun wanda zai gaje shi.
Firayim Minista Akiiki ya bayyana cewa marigayin yana da wanda zai gaje shi, kuma zai bayyana sunansa a lokacin da ya dace bisa tsari da al’adun masarautar Tooro.
Rasuwar Sarki Oyo ta sanya sauran masarautun kasar Uganda cikin alhini, inda Masarautar Buganda mafi girma da fada aji a kasa ta aike da sakon ta’aziyya ga al’ummar Tooro, tare da yaba irin gudunmowar da gidan sarautar ya bayar ga raya al’adu da zamantakewar al’ummu daban-daban na kasar.