Majalisar Dattawa ta bukaci Gwamnatin Tarayya ta kwace lasisin wasu kamfanonin Afirka ta Kudu da suke kasuwanci a Najeriya.
Wannan bukata ta biyo bayan kiran da dan Majalisar Dattawa mai wakiltar mazabar Edo ta Arewa, Sanata Adams Oshiomhole, ya yi ne yayin zaman Majalisar na ranar Talata, 5 ga watan Mayu.
Sanata Oshiomhole, wanda ya ce lokacin zubar da hawaye da jajantawa ya wuce yanzu lokaci ne na mayar da raddi irin wanda diflomasiyya ta tanada, ya yi kra ga Majalisar da ta umarci Gwamnatin Tarayya ta dauki tsauraran matakan tattalin arziki a kan kamfanonin Afirka ta Kudu da suke kasar nan ne sakamakon sabon tashin hankali da hare-haren kyamar baki da ake kai wa ‘yan Najeriya a can.
- ADC ta karbe shugabancin marasa rinjaye a Majalisar Dattawa
- Kare ‘yancin ‘yan jarida hakki ne a wuyan mu –Ministan Yada
- Yadda Kwankwaso da Obi suka yi wuf suka yanki katin NDC
Tsohon Shugaban na Kungiyar Kwadagon ta Najeriya (NLC) ya ba da shawarar cewa ya kamata a mayar da MTN mallakin Najeriya, sannan a soke lasisin kamfanin Multichoice, mammallakin DSTV, kamfanonin da ya ce suna fitar da miliyoyin daloli daga Najeriya a kullum, yayin da ‘yan Najeriya suke fuskantar muzgunawa a kasar da wadannan kamfanoni suka fito.
“Wannan Majalisar ya kamata ta dauki matsayar cewa MTN, kamfanin Afirka ta Kudu da ke kwashe miliyoyin daloli daga Najeriya kowace rana, a karbe shi ya koma na kasa sannan a soke lasisinsa,” in ji Oshiomhole.
Bukatar ta samu goyon baya daga dan majalisa mai wakiltar Anambra ta Tsakiya, Sanata Victor Umeh, wanda ya bayyana damuwarsa kan yadda ‘yan Najeriya suke rayuwa cikin fargaba.
Ya ce abin takaici ne yadda Afirka ta Kudu take bin Najeriya da sharri, bayan rawar da ta taka wajen yaki da wariyar launin fata a kasar.
Umeh ya yi kira ga Kungiyar Tarayyar Afirka (AU) ta tsoma baki tare da sanya wa Afirka ta Kudu takunkumi kafin lamarin ya kai ga kazancewa.
Wannan matsin lamba daga bangaren Majalisa na zuwa ne a daidai lokacin da al’ummar Najeriya suke jiran ganin wani kwakkwaran mataki daga Gwamnatin Tarayya don kawo karshen cin zarafin ‘yan kasa dake zaune a kasashen waje.
Rahotanni sun nuna cewa ‘yan Najeriya na fuskantar barazana a wasu kasashen Afirka, da suka hadar da Afirka ta Kudu da kuma Libya, yayin da a Ghana ake samun takun saka game da dokoki da suka shafi kananan sana’o’i da aka haramta wa ‘yan kasashen waje mazauna kasar.
