Mutane huɗu sun tsallake rijiya da baya bayan da suka shafe sa’o’i a ƙarƙashin wani gini mai hawa uku da ya ruguje a yankin Popo-Giwa da Masalasi Gogoro, da ke kusa da hanyar Aikobi a ƙaramar hukumar Ilorin a jihar Kwara.
Rahotanni sun ce ginin ya ruguje ne da misalin ƙarfe 5:30 na safiyar Talata, lamarin da ya jefa mazauna yankin cikin firgici.
An yi zargin cewa akwai mutane a cikin ginin a lokacin da ya ruguje, musamman ganin cewa mafi yawan mutanen yankin suna barci a lokacin.
Rahotanni sun ce an mika waɗanda aka ceto asibiti domin a duba lafiyarsu, ko da yake ba a bayyana sunayensu ko irin raunin da suka samu ba.
Sai dai ana fargabar cewa wasu mutane akalla takwas na iya kasancewa a ƙarƙashin baraguzan ginin, har yanzu ba a tabbatar da ainihin adadin mutanen da ke cikin ginin lokacin da ya ruguje ba, yayin da jami’an ceto ke ci gaba da bincike domin gano waɗanda ka iya tsira.
Ma’aikatan hukumar kashe gobara ta jihar Kwara, da jami’an Hukumar Tsaron Fararen Hula ta Najeriya (NSCDC), da kuma Hukumar Agajin Gaggawa ta jihar Kwara, sun yi sansani a wajen, domin tabbatar da tsari da oda.
Har yanzu ba a bayyana musabbabin rugujewar ginin ba, sai dai yayin da hukumomi ke gudanar da bincike, wasu na dora alhakin rugujewar akan tsarin gini, amfani da kayan da ba su da inganci, rashin kyakkyawan tsari da ka’idoji ka iya kaiwa ga musabbabin abinda ya jawo rushewar.