Rundunar ’Yan Sandan Babban Birnin Tarayya (FCT) ta kama mutane bakwai da ake zargi da aikata laifukan da suka shafi miyagun kwayoyi a yankin Lobito Crescent, Wuse 2, Abuja.
A cikin wata sanarwa da Jami’ar Hulda da Jama’a ta Rundunar ’Yan Sandan FCT, SP Josephine Adeh, ta fitar, ta ce jami’an rundunar da ke aiki karkashin Sashen ’Yan Sandan Maitama sun gudanar da samamen ne a ranar 2 ga Satumba, 2026.
Adeh ta ce wadanda aka kama sun hada da maza shida da mace daya, wadanda ake zargi da hannu a laifukan da suka shafi miyagun kwayoyi.
- Masu satar danyen mai sun mutu a Ribas
- Babu ruwan DSS da abinda ke tsakanin farar hula-Ajayi
- An kama ‘yan ƙasar Sin huɗu kan hakar ma’adinai a Neja
Ta bayyana cewa jami’an sun samu busassun ganyaye da ake zargin tabar wiwi (Cannabis) ne, kwayoyin Tramadol, kwalbar Codeine, da wata bakar leda dauke da busassun ganyaye da ake zargin Cannabis sativa ne.
A cewar sanarwar, wadanda ake zargin suna hannun ’yan sanda yayin da ake ci gaba da gudanar da bincike, kuma za a gurfanar da su a gaban kotu bayan kammala binciken.
Rundunar ta yi kira ga mazauna Abuja da su guji duk wani nau’in aikata laifi, musamman shaye-shayen miyagun kwayoyi da safararsu.
Haka kuma, ta bukaci jama’a da su kasance masu lura da harkokin tsaro tare da kai rahoton duk wani mutum, aiki ko wuri da ake zargi zuwa ofishin ’yan sanda mafi kusa.