Za a gudanar da Taron Ƙasashen Duniya kan Iska Mai Tsabta a birnin Istanbul na Turkiyya daga ranar 23 zuwa 24 ga Satumba, 2026.
Taron zai haɗa wakilan gwamnatoci daga sassa daban-daban na duniya, ƙungiyoyin ƙasa da ƙasa, jami’o’i, cibiyoyin bincike da ƙungiyoyin fararen hula domin musayar hanyoyin rage gurɓatar iska da ƙarfafa haɗin gwiwa.
Hukumar Tattalin Arziƙi da ta Muhalli na Majalisar Ɗinkin Duniya (UNECE), UNEP, da hadin gwiwar gwamnatin Turkiyya ne suka shirya taron tare.
Mahalarta taron za su tattauna sauyin yanayi da gurɓatar iska a duniya, illolin da ƙalubalen manufofi, nazarin dokoki da fasahohi da za su taimaka wajen kare lafiyar jama’a, muhalli da rage tasirin sauyin yanayi.
Taron na kwanaki biyu, zai mayar da hankali ne kan binciken kimiyya da manufofin gwamnati, rage hayaƙin da motocin sufuri ke fitarwa, samar da kuɗaɗen aiwatar wa da kuma yadda za a isar da sakon muhimmancin ingancin iska ga jama’a
Taron na da nufin ƙara wayar da kan jama’a game da sabbin matsalolin gurɓatar iska, musayar hanyoyin magance matsalar da za su taimaka wa yanayi da ci gaba mai ɗorewa, da kuma ƙarfafa haɗin gwiwar ƙasashe wajen sa ido da kula da ingancin iska. Haka kuma, za a tsara matakan da za a iya aiwatarwa a matakin duniya, yanki da ƙasa.
A ranar 1 ga Maris, a taron Majalisar Ɗinkin Duniya kan Muhalli karo na shida, aka amince da ƙudurin da ke kira da a ƙarfafa haɗin gwiwa, Ƙudurin ya kuma bukaci ƙasashe su kafa manufofi da ƙa’idoji, da suka dace da na Hukumar Lafiya ta Duniya (WHO).