Shugaban China, Xi Jinping, ya bayyana ƙungiyar BRICS a matsayin dandalin da ya fi tasiri a duniya wajen haɗin gwiwa tsakanin ƙasashe masu tasowa da kasuwannin ƙasashe masu tasowa, tare da kira ga ƙungiyar da ta taka rawar da ta dace wajen samar da zaman lafiya a Yammacin Asiya.
Da yake jawabi a taron BRICS da aka fara gudanar a yau, a New Delhi, Xi ya ce China za ta yi aiki tare da ƙasashe mambobin BRICS domin samar da zaman lafiya da kwanciyar hankali a Yammacin Asiya da yankin Gulf.
Kamfanin dillancin labarai na Xinhua na China ya ruwaito Xi yana cewa, yayin da yanayin tsaro a Yammacin Asiya da yankin Gulf ke ci gaba da sauyawa, yaƙin da ake yi a yankin ya haddasa asara mai yawa ga al’ummomin yankin, kuma bai amfani muradun bai ɗaya na ƙasashen duniya ba.
- Shugabannin BRICS sun nuna damuwa kan harajin bai ɗaya na WTO
- ƙungiyar BRICS ta amince da yarjejeniyar New Delhi
- Taron Kungiyar BRICS: Abubuwan da za a tattauna da muhimmancin su
Xi ya yi kira ga shugabannin manyan ƙasashe masu tasowa da su taka rawar da ta dace wajen samar da zaman lafiya a Yammacin Asiya, tare da buƙatar ƙasashe mambobin BRICS su tsaya a kan abin da ya dace a tarihi.
Ya ce ƙasashen BRICS ya kamata su yi adawa da tunanin Yaƙin Cacar Baki, tare da yin Allah-wadai da take ikon mallakar wasu ƙasashe da kuma tsoma baki cikin harkokinsu na cikin gida.
Shugaban China ya kuma ce ƙasashen BRICS ya kamata su ƙara ƙarfafa haɗin gwiwa a fannin ƙiƙirarriyar fasahar (AI) domin amfani da ita wajen inganta sabbin masana’antu a tsakanin ƙasashen ƙungiyar.
Xi ya bukaci ƙasashen BRICS su jagoranci ƙoƙarin samar da tsarin shugabancin duniya a fannonin sararin samaniya ta intanet, da kuma teku, tare da ƙara ƙarfafa muryar ƙasashen Kudancin Duniya.
Ya ce ƙasashen BRICS ya kamata su kasance a sahun gaba wajen samar da sabbin hanyoyin ci gaba, da kuma tabbatar da zaman lafiya da kwanciyar hankali, tare da ƙarfafa musayar ilimi da fahimtar juna tsakanin al’ummomi daban-daban.
Xi ya kuma jaddada cewa ƙasashen mambobin ƙungiyar ya kamata su mayar da hankali wajen inganta tsarin shugabancin duniya, yana mai cewa BRICS ya kamata ta taimaka wajen karkatar da tsarin ƙasa da ƙasa zuwa ga mafi girman adalci da daidaito, tare da yin aiki tare domin gina al’ummar duniya mai makoma ɗaya.