Yawancin gidajen man fetur a yankin Birnin Tarayya, Abuja, suna ci gaba da kara farashin litar man fetur saboda karin N85 da matatar mai na Dangote ya yi, daga N1,265 zuwa N1,350 ga kowace lita, a daidai lokacin da farashin danyen mai a duniya ya yi tashin gwauron zabi.
Danyen mai wanda shi ne abin da ake amfani da shi wajen tantance farashin mai na Najeriya, ana sayar da shi akan kimanin dala 107.92 a kowace ganga, sannan yanzu ya kai dala 108.21 a kowace ganga.
Wannan karin ka iya shafar farashin sufuri da kuma ababen masarufi.
Wani binciken da Kamfanin Dillancin Labarai na Najeriya, NAN, ya yi ranar Lahadi a Abuja ya nuna cewa wasu gidajen man fetur sun fara kara farashin litar fetur, inda masu ababen hawa ke biyan kudi fiye da yadda suka saba.
-
Gobara ta jikkata mutane shida a wata masana’antar kayan wasanni a Indiya
-
Kashim Shettima ya jaddada aniyar Nijeriya ta gudanar da aiki da WTO
-
Najeriya da Benin sun ƙarfafa harkokin kasuwanci
A cewar NAN, gidajen mai na MRS sun kara farashin litar daga N1,350 zuwa N1,395, yayin da gidan man NIPCO suka kara farahin litar daga N1,350 zuwa N1,430.
Gidajen man Mobil ma sun kara daga N1,350 zuwa N1,400 ga kowace lita.
Wata ma’aikaciya a gidan man fetur na MRS, wadda ta bukaci a sakaya sunanta, ta ce farashin litar man ka iya kara hawa daga gobe.
“A halin yanzu muna sayar da tsohon kayan da muke da shi kan N1,395 ga kowace lita, amma daga gobe, da zarar sabon kaya ya iso, farashin zai kara hawa,” in ji ta.
Dr Aliyu Ilias, masanin tattalin arziki, ya ce karin farashin litar man fetur na baya-bayannan na iya kara tsananta hauhawar farashi da kuma zurfafa wahalar tattalin arziki ga ‘yan Najeriya.
“Yadda farashi ke kara hauhawa, haka farashin ababen masarufi zasu kara hauhawa, musamman kayan abinci, domin komai yana da alaka da kudin sufuri.
“Wannan irin sauyi ba shi da kyau ga tattalin arziki kwata-kwata, kuma mutane za su fuskanci karin wahala sakamakon haka,” in ji shi.
Sakataren Yada Labarai na Kasa na Kungiyar Dillalan Man Fetur ta IPMAN, Chinedu Ukadike, ya ce ‘yan kasuwa sun sake duba farashinsu litar mai sakamakon karin da matatar Dangote ta yi a jere a jere.
Ukadike ya ce sauye-sauyen farashi akai-akai na haifar da rashin tabbas ga ‘yan kasuwa da masu amfani da man.