Amnesty ta ce hukumar Birnin Tarayya Abuja ta take hakkin mazauna Durumi

Kungiyar kare hakkin dan Adam ta kasa-da-kasa, Amnesty International, ta nuna damuwarta game da rahotannin da ke cewa hukumomi sun fara korar Fulani makiyaya sama da 1,500 daga Jihar Kwara zuwa wasu jihohin Arewa.

Kungiyar ta ce korar mutane da karfi a cikin kasarsu ya saba wa dokokin jin kai na kasa-da-kasa, a saboda haka ta ke kira ga mahukunta da su duba halin da wadannan mutane ke ciki domin kare hakki da mutuncin su.

Amnesty International tace yawancin su a jihar kwara aka haife su, har suka girma, amma Gwamnatin Jihar ta hana su hakkinsu na zama a jihar su ta haihuwa kamar yadda kundin tsarin mulkin kasa ya tanadar.

“A makon jiya sojoji sun yi mana rajista tare da tambayar mu jihar da muke son komawa- Da yawa mun zabi Neja da Zamfara saboda tsoro- Mu duka ‘yan jihar Kwara ne.

Kwashe mu zuwa wani waje ya saba wa son zuciyar mu, amma ba mu da yadda za mu yi.” Inji wani makiyayi da abin da ya shafa.

An fara kwashe makiyayan tun a makon da ya gabata zuwa jihohin Kaduna, Kano, Abuja, Taraba, Neja, da Zamfara, bayan basu zabin inda suke bukatar komawa.

Ya zuwa Lahadi 10 ga Mayu, 2026, rukunin farko a motoci biyar sun isa garin Gusau, inda suka tarar da rashin kyakkyawar tarba, lamarin da ya jefa su cikin sabon yanayi na gudun hijira.

Kungiyar ta Amnesty ta ce makiyayan sun kwashe tsawon watanni a tsare a wani sansanin ‘yan bautar kasa dake yanking Yikpata na jihar ta Kwara ba tare da hakki ba, suna kuma cikin tsananin bukatar agajin gaggawa.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *