Wakilin MSF a Najeriya Dokta Ahmed Aldikhari ya ce kungiyar tana aiki da masu ruwa da tsaki don magance matsalar (Hoto: Isah Ismaila/HumAngle)

Kungiyar likitoci ta Médecins Sans Frontières (MSF) ta ce Najeriya ce ta fi kowace kasa yawan masu fama da laulurar tamowa a shekarar 2025.

Wakilin kungiyar a Najeriya, Dokta Ahmed Aldikhari, ya bayyana hakan yayin kaddamar da Rahoton Ayyukan Kungiyar na 2025 a Abuja.

“Tamowa na cikin manyan matsalolin da muka gani a Najeriya.

“Yawan masu fama da ita a Najeriya shi ne mafi girma a duniya, kuma muna aiki a kasashe 77,” inji Aldikhari.

Ya kara da cewa MSF tana hada gwiwa da Gwamnatin Najeriya da kungiyoyi masu zaman kansu don magance matsalar.

Ya ce sauyin yanayi da rashin tsaro (musamman a jihohin Arewa wadanda ake kallo a matsayin rumbun abincin kasar) da rashin ababen more rayuwa da karancin kayan aiki a asibitoci da karancin ma’aikata da karancin albashi da kuma rashin isassun kudade ne suka haddasa wannan mummunan hali.

Abubuwan da rahoton ya kunsa

Rahoton na MSF na shekarar 2025 ya mayar da hankali a kan karuwar tamowa da barkewar annoba a-kai-a-kai, da kuma matsalolin da suke dakushe lafiyar mata masu juna biyu.

Rahoton ya ce tun daga shekarar 2022 ake samun karuwar tamowa a Arewacin Najeriya, amma shekarar 2025 ce mafi muni.

“Alkaluman shekarar 2025 suna da ban tsoro,” in ji Aldikhari.

Ya ce tamowa na saurin haddasa wasu cututtuka kamar kyanda da zazzabin cizon sauro da sankarau, musamman idan babu asibiti a kusa.

Rahoton ya ce yara 353,989 ne suka samu maganin tamowa mai tsanani a wajen asibiti, yayin da aka kwantar da yara 90,723 wadanda suka fuskanci wasu matsalolin lafiya sanadiyyar tamowar.

Kungiyar ta ce ta yi wa yara sama da 440,000 maganin tamowa, yayin da mutum sama da 300,000 da suka yi fama da zazzabin cizon suka samu magani.

Ta kuma ce ta taimaka wa mata 33,500 yayin haihuwa.

 

MSF ta ce a shekarar 2025 ta gudanar da ayyuka a jihohi goma da suka hada da: Bauchi da Borno da Kuros Riba da Ebonyi da Jigawa da Kano da Katsina da Kebbi da Sakkwato da Zamfara, sannan ta kafa sabon ofis a Kaduna.

Haka kuma, ta kai daukin gaggawa a jihohin Neja da Adamawa.

Lafiyar Mata Da Annoba

Rahoton ya nuna cewa Najeriya na ci gaba da fuskantar annobar cututtuka kamar kwalara da zazzabin Lassa da kyanda da sankarau da typhoid.

A shekarar 2025 kadai, inji rahoton, MSF ta yi wa yara 38,753 maganin kyanda, sannan ta yi wa mutun 6,123 maganin sankarau.

Game da lafiyar mata kuwa, Najeriya na cikin kasashen da mata suke mutuwa sosai yayin haihuwa.

Mata a yankunan karkara suna fuskantar nisan asibiti da rashin sufuri da tsadar magani.

MSF ta ce ta gudanar da tiyatar yoyon fitsari ga mata 224 a shekarar.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *