Gwamnatin Jihar Kaduna, ta ce ta kwato sama da hekta 500,000 na gonaki da ‘yan bindiga suka mamaye cikin shekaru uku da suka gabata, sakamakon ingantuwar tsaro da ya bai wa manoma damar komawa gonakinsu.
Kwamishinan Yada Labarai da Al’adu na jihar, Ahmed Maiyaki, ne ya bayyana hakan ranar Lahadi, a wani taron liyafar dare da Kungiyar Wakilan Kafofin Yada Labarai ta Jihar Kano ta shirya a Kaduna, a matsayin wani bangare na taron shekara-shekara na kungiyar.
- Tinubu ya isa Paris don ci gaba da hutun shekara a Turai
- ‘Yan bindiga sun kashe makiyaya uku da shanu 50 a sabon harin Jihar Filato
- Tsohon Shugaban Jam’iyyar PDP na Kasa, Bamanga Tukur, ya rasu
Ya ce matakan da gwamnatin jihar ta dauka domin magance matsalar rashin tsaro sun haifar da gagarumar nasara a fannoni daban-daban.
Maiyaki, ya tuna cewa a baya ‘yan bindiga sun mamaye wasu yankunan karkara, inda suke karbar haraji, da kayyade yadda za a gudanar da aikin noma.
Ya ce lamarin ya yi tsanani har manoma suka kasa zuwa gonakin su, amma yanzu zaman lafiya ya dawo sakamakon tsarin tsaron da gwamnatin ta bullo dashi wanda al’umma ke jagoranta da kuma hanyoyin gano barazana tun da wuri, lamarin da ya bai wa manoma damar komawa gonakinsu.
Jihar Kaduna ta sha fama da matsalolin tsaro da dauke da mutane domin karbar kudin fansa, lamarin da a baya bayan ke ja da baya sannu a hankali.