Mataimakin Shugaban Ƙasa, Kashim Shettima, ya isa birnin Yola na Jihar Adamawa, inda ya jagoranci tawagar gwamnatin tarayya domin kai ziyarar ta’aziyya ga iyalan marigayi dattijo kuma tsohon ɗan siyasa, Bamanga Tukur, bisa umarnin Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu.
Gwamnan Jihar Adamawa, Ahmadu Umaru Fintiri, tare da mambobin majalisar zartarwar jihar, ne suka tarbi Mataimakin Shugaban Ƙasar a lokacin da ya isa Yola.
- Messi zai sake buga wa Argentina wasa kafin yin bankwanan ƙarshe
- Kwallon Raga: Najeriya ta samu nasara ta farko a Gasar Ƙasashen Afirka ta 2026
- Taron NFF: Tawagar FIFA da CAF ta kammala tattara bayanai ta koma Zurich
Tawagar ta ƙunshi Mataimakin Shugaban Jam’iyyar APC na Ƙasa mai kula da Arewa, Ali Bukar Dalori; tsohon Ministan Sufuri, Sanata Sa’idu Ahmed Alkali; Mataimakin Shugaban Ma’aikata na Shugaban Ƙasa a Ofishin Mataimakin Shugaban Ƙasa, Sanata Ibrahim Hassan Hadejia, da sauran manyan jami’an gwamnati.
Marigayi Bamanga Tukur ya taɓa zama Gwamnan tsohuwar Jihar Gongola, sannan ya zama Shugaban Jam’iyyar PDP na Ƙasa. Ya kuma kasance fitaccen ɗan kasuwa, tare da taka muhimmiyar rawa a harkokin gwamnati da kasuwanci a Afirka tsawon shekaru da dama.