Wani dalibin tukin jirgi da mai koyar da shi sun mutu a ranar Juma’a, bayan ƙaramin jirgin da suke amfani da shi wajen atisayen tuka jirgi ya yi hatsari a kudancin Kenya, kamar yadda ‘yan sanda suka bayyana.
Jirgin ya faɗo ne kusa da injinan samar da wutar lantarki daga iska a yankin Kipeto, wani yanki mai tuddai da ke gundumar Kajiado, kudu maso yammacin Nairobi, a cewar kwamandar ‘yan sandan Kajiado West, Maureen Kuto.
- Filato: ‘Yan Sanda sun kama mutum 34, sun kwato bindigogi 10 da harsasai 54
- Yara kanana da ake zargi da haƙar ma’adinai ba bisa ƙa’ida ba sun mutu a hannun Hukumar Tsaro ta NSCDC a Jihar Neja
- Atiku ya soki gwamnatin Tarayya kan tsadar rayuwa
Ba a bayyana sunayen mutanen biyu da suka rasu nan take ba.
Hotunan bidiyo daga wurin da hadarin ya faru sun nuna jirgin ya tarwatse zuwa manyan sassa da dama a cikin wani fili mai busasshiyar ciyawa.
Shaidun gani da ido da jaridar The Associated Press (AP) ta tattauna da su sun ce hazo mai yawa da aka samu da safiyar ranar ya rage gani a yankin.