Tobi Amusan ta Najeriya ta kammala kakar wasannin guje-guje da tsalle-tsalle a matsayi na biyu a tseren mita 100 na shingen mata a Gasar Athlos ta 2026 da aka gudanar a London.

Amusan ta yi gudu na minti 12 da dakika 5, wanda shi ne mafi kyawun kokarinta a wannan kakar.

‘Yar wasan Amurka, Alaysha Johnson, ta doke Amusan, ‘yar Najeriya da kasa da dakika 0.01 kacal ta lashe gasar.

Matsayi na biyu da Amusan ta samu ya ba ta kyautar kudi dala 35,000, yayin da ta kammala kakar gasar wanda ya dau zafi da kuma hankulan al’umma na duniya.

Wannan sakamakon ya kawo karshen kakar wasan Amusan ta 2026, inda taurariyar Najeriyarp ta sake nuna bajinta a cikin manyan ‘yan tseren na mita 100 a duniya.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *