Tawagar Kwallon Raga ta kasa ta farko ta Najeriya, Green Hawks, za ta shiga filin wasa ranar Asabar, inda za ta kara da mai masaukin baki, Kenya, a Gasar Cin Kofin Afirka na Kwallon Raga tare kuma da neman gurbin shiga Gasar Cin Kofin dtuniya ta 2027.
Najeriya ta isa Nairobi ranar Jumma’a, 18 ga Satumba, inda ta nufi Otal din tawagar kai tsaye, yayin da ‘yan wasan suka huta kadan kafin su ka maida hankali kan aikinsu na farko.
Green Hawks za ta fuskanci Kenya da karfe 4:00 na yamma agogon Najeriya, ranar Asabar, 19 ga Satumba, a Cibiyar Wasanni ta Kasa da Kasa ta Moi, Kasarani.
Jadawalin Hukumar Gasar Kwallon Raga ta Duniya ya tabbatar da wasan a matsayin bude rukuni na 2 na Najeriya.
- Gasar Cin Kofin Duniya na Mata: Najeriya za ta kara da Colombia a wasan kwata-fainal
- Gasar AFCON 2027: An gayyaci Ndidi da Osimhen da Iwobi da wasu 21 don wasan neman tikiti
- Brentford ta lallasa Chelsea da ci 3-0 a wasan mako na biyar
.
Ga Najeriya, wannan lokaci ba kawai yana nufin wasan budewa ba ne.
Lokaci ne mai cike da dimbin tarihi da kuma ci gaba ga harkar wasanni a kasar.
Babbar kocin Tawagar, Alison Akinrinsola, ta bukaci wannan tarihi mai muhimmancin gaske da ya zaburar da ‘yan wasanta maimakon ya dauke musu hankali.
Kafin zuwan su Kenya, tawagar ta gudanar da shirye-shiryen ta a Landan, inda ta fara gwada karfinta akan Jamaica, da Pakistan da kuma ScotlanBayan ta fafata da Kenya, Najeriya za ta hadu da Uganda da karfe 6 na yamma ranar Lahadi.
Sannan kuma a ranar 20 ga Satumba, za ta fuskanci Malawi da karfe 4 na yamma.
Har wayau, a ranar Litinin, 21 ga Satumba, Najeriya za ta kara da Zambia da karfe 2 na yamma, sai kuma a ranar Talata, 22 ga Satumba za ta kammala jadawalin rukuni na 2.
Tawagun mata goma ne ke fafatawa a Nairobi, kuma gasar ta zama hanyar neman gurbin shiga Gasar Cin Kofin Duniya ta Kwallon Raga ta 2027 da za a yi a Sydney. Afirka ta Kudu da Uganda sun riga sun samu gurbin shiga gasar ta hanyar matsayinsu a duniya, yayin da gasar za ta tantance kasashe biyu na gaba na Afirka da suka cancanci gayyatar zuwa Sydney.