Babban Hafsan Rundunar Sojin Sama ta Najeriya (NAF), Air Marshal Sunday Kelvin Aneke, ya jagoranci tawagar rundunar zuwa kamfanin Bell Textron da ke Amarillo, Texas, a Amurka, domin sanya hannu kan yarjejeniyar sayen jirage masu saukar ungulu guda 12 kirar AH-1Z Viper na kai hari.
Daraktan Hulda da Jama’a da Yada Labarai na NAF, Air Commodore Ehimen Ejodame, ne ya bayyana hakan a cikin wata sanarwa da ya fitar ranar Litinin.
- Sojojin ‘Operation Enduring Peace’ sun ceto mutane biyu da Aka sace a filato
- NSCDC ta tsare jami’ai 24 kan mutuwar masu hakar ma’adinai 33 a Neja
- ‘Yan uwan mijin da ake zargin matarsa ta kashe shi saboda zai mata kishiya na neman a yi adalci
Ejodame ya ce wannan mataki na daga cikin muhimman abubuwan da ake aiwatarwa karkashin shirin hadin gwiwar tsaro tsakanin gwamnatocin Najeriya da Amurka, da kuma kokarin gwamnatin tarayya na zamanantar da rundunar sojin kasar.
Ya ce sayen jiragen na daga cikin hangen nesan gwamnatin tarayya na karfafa tsarin tsaro da kariyar Najeriya, tare da samar wa rundunar sojin kasar kayan aiki da dabarun da za su ba ta damar tunkarar barazanar tsaro da ke akwai da kuma sabbin barazanar da ka iya tasowa.