Gwamnatin Tarayya ta ce ba za ta kare duk wani jami’in da bincike ya gano yana da hannu wajen mutuwar mutane 37 da suka rasu a hannun Hukumar Tsaron Fararen Hula ta Najeriya (NSCDC) a Jihar Neja ba.

Ministan Harkokin Cikin Gida, Olubunmi Tunji-Ojo, ya bayyana hakan yayin ƙaddamar da kwamitin bincike mai zaman kansa mai mambobi 10 a Abuja, bisa umarnin Shugaba Bola Ahmed Tinubu.

Kwamitin zai binciki yadda aka kama da tsare mutanen, tare da gano musabbabin mutuwarsu ta hanyar binciken lafiya da na kimiyya.

Haka kuma kwamitin zai tantance ko sakaci ko rashin ɗa’a ko haɗin baki ko karya aikin da ya rataya kan jami’ai ya faru.

Ministan ya umarci NSCDC da sauran jami’an da abin ya shafa su miƙa dukkan takardu da hujjojin da suka shafi lamarin. Ya kuma gargadi duk wanda ya lalata ko ɓoye hujja, tsoratar da shaidu ko ƙoƙarin hana binciken gudanar da aikinsa cewa za a ɗauki matakin doka a kansa.

Kwamitin, ƙarƙashin jagorancin tsohon babban jami’in DSS, Jonathan Kure, zai fara aiki nan take kuma ana sa ran zai gabatar da rahotonsa cikin makonni biyu.

By Bashar Muhammad Dange

Bashar Muhammad is a Nigerian multimedia journalist, broadcaster, producer, and media professional with years of experience in radio broadcasting, reporting, and content creation. He holds a B.Sc. in Mass Communication from Ahmadu Bello University, Zaria, and a Diploma in Mass Communication from The Polytechnic of Sokoto. Throughout his career, Bashar has produced and presented programmes on current affairs, agriculture, health, education, and community development. He has worked with leading media organizations including Garkuwa FM 95.5 Sokoto, Trimming Radio 96.5 FM Goronyo, Giantability Media Network, and ABU Samaru FM. As a journalist and presenter, he has conducted interviews, reported on social and developmental issues, and amplified the voices of underserved communities. Beyond broadcasting, Bashar has demonstrated leadership in media management, programme development, and team coordination. He has received several awards and recognitions for his contributions to journalism, Hausa language development, and community service. His expertise includes radio production, news reporting, sound editing, investigative journalism, media analysis, and public presentation. Driven by a passion for impactful storytelling and public service, Bashar Muhammad continues to use journalism and media platforms to inform, educate, and empower communities across Nigeria.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *