Mataimakin Shugaban Ƙasa Kashim Shettima ya shiga cikin shugabannin duniya wajen buɗe babban taron Majalisar Ɗinkin Duniya karo na 81, UNGA, da ke gudana a birnin New York.

Shettima, wanda ke wakiltar Shugaba Bola Ahmed Tinubu tare da jagorantar tawagar Najeriya, zai gabatar da jawabin Najeriya a ranar Alhamis, 24 ga Satumba, inda zai bayyana matsayinta kan manyan batutuwan duniya da manufofin Najeriya.

Taron na bana, wanda ke gudana daga 22 zuwa 28 ga Satumba, na ƙarƙashin taken “Maido da amana, tafiyar da sauyi: Majalisar Ɗinkin Duniya da ke samar da sakamako ga kowa”, tare da halartar shugabannin ƙasashe daban-daban.

A yayin tarukan da ya halarta a New York, Shettima ya kuma yi kira ga ƙasashen Afirka da su daina dogaro da fitar da albarkatun ma’adinai danye, su mayar da hankali kan sarrafa su da samar da masana’antu domin ƙirƙirar ayyukan yi da bunƙasa tattalin arziki.

Shettima ya ce Najeriya za ta yi amfani da taron wajen bayyana muradunta da ƙarfafa haɗin gwiwa da sauran ƙasashe kan zaman lafiya da tsaro da ci gaba mai ɗorewa da sauyin yanayi da gyaran tsarin tattalin arzikin duniya.

By Bashar Muhammad Dange

Bashar Muhammad is a Nigerian multimedia journalist, broadcaster, producer, and media professional with years of experience in radio broadcasting, reporting, and content creation. He holds a B.Sc. in Mass Communication from Ahmadu Bello University, Zaria, and a Diploma in Mass Communication from The Polytechnic of Sokoto. Throughout his career, Bashar has produced and presented programmes on current affairs, agriculture, health, education, and community development. He has worked with leading media organizations including Garkuwa FM 95.5 Sokoto, Trimming Radio 96.5 FM Goronyo, Giantability Media Network, and ABU Samaru FM. As a journalist and presenter, he has conducted interviews, reported on social and developmental issues, and amplified the voices of underserved communities. Beyond broadcasting, Bashar has demonstrated leadership in media management, programme development, and team coordination. He has received several awards and recognitions for his contributions to journalism, Hausa language development, and community service. His expertise includes radio production, news reporting, sound editing, investigative journalism, media analysis, and public presentation. Driven by a passion for impactful storytelling and public service, Bashar Muhammad continues to use journalism and media platforms to inform, educate, and empower communities across Nigeria.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *