Hukumar Ƴansandan Najeriya ta sanar da tura aƙalla Kwamishinonin Ƴansanda (CPs) 30 da jami’ai fiye da 15,000 domin zaɓen gwamna da za a yi ranar Asabar a Jihar Osun.
Kakakin Hukumar Ƴansanda na Ƙasa, CSP Anietie Iniedu, shi ne ya bayyana haka lokacin da yake yi wa manema labarai bayani a Osogbo, babban birnin Jihar Osun, game da shirye-shiryen ƴansanda na zaɓen gwamnan. Gwamna Ademola Adeleke na Jam’iyyar Accord, Bola Oyebamiji na Jam’iyyar All Progressives Alliance, da ɗan takarar Jam’iyyar African Democratic Congress, Najeem Salaam, suna cikin manyan masu fafitikar neman babban kujerar siyasar jihar.
“Mun tura ƴansandan kwantar da tarzoma masu ɗauke da makamai zuwa kowace ƙaramar hukuma a jihar. Don haka, muna da rundunoni 30 a faɗin ƙaramomin hukumomi 30. Kowace runduna tana da kusan ƴansanda 60.”
Iniedu ya ce ƴansanda sun fara tura jami’ai da kayan aiki don zaɓen tun makwanni uku kafin ranar zaɓen, inda ya ƙara da cewa an tsara tsare-tsaren ne domin samar da tsaro a dukkan ƙaramomin hukumomi 30 na jihar. A cewarsa, za a tura jami’an ƴansanda fiye da 15,000 don ayyukan zaɓe, yayin da rukunin helikafta da na drones na ƴansanda tuni suka isa jihar don tallafa wa aikin sa ido.
Haka kuma, ya bayyana cewa an tura rundunoni biyu na Ƴansandan Kwantar da Tarzoma (PMF), inda kowace runduna ke ɗauke da jami’ai fiye da 60, zuwa shalkatar Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta Ƙasa (INEC) da ke Osogbo. Haka zalika, ya ce kowace ƙaramar hukuma cikin guda 30 da ke jihar za ta sami runduna ɗaya ta ƴansandan kwantar da tarzoma don ƙarfafa tsaro lokacin zaɓen.
“Haka kuma muna da rundunoni biyu na ƴansandan kwantar da tarzoma masu ɗauke da makamai da aka tura zuwa shalkatar INEC da ke nan Osogbo. Jami’an da ke zama a ƙaramomin hukumomin, wani Kwamishinan Ƴansanda ne ke daidaita aikinsu. Akwai Kwamishinan Ƴansanda guda ɗaya a kowace Ƙaramar Hukuma.”
“Haka kuma muna da Mataimakin Kwamishinan Ƴansanda (DCP) guda ɗaya a kowace Ƙaramar Hukuma, da kuma Kwamandan Mopol da Kwamandan PMF mai muƙamin Mataimakin Kwamishinan Ƴansanda (ACP) a kowace Ƙaramar Hukuma.”
“Har zuwa ranar Alhamis, rukunin helikafta da na drones ɗinmu sun riga sun isa Osogbo, kuma za su riƙa gudanar da aikin sa ido a yankunan tun daga yanzu, lokacin zaɓe, da kuma daɗewar da za a yi bayan an kammala zaɓukan.”
Kakakin ƴansandan ya kuma ce Rundunar Soji za ta datse iyakokin da ke shiga Jihar Osun daga tsakar daren ranar Asabar a matsayin wani ɓangare na matakan taƙaita zirga-zirga lokacin zaɓen.
“Za mu kulle jihar baki ɗaya. Ba za mu ƙetare wa kowace mota zirga-zirga ba, in ban da waɗanda ke kan ayyuka na musamman, ayyukan tsaro, da kuma waɗanda ke fita don kaɗa ƙuri’unsu,” in ji shi.
Iniedu ya buƙaci iyaye da su gwaɗatar da ƴaƴansu da su guji tafka laifukan zaɓe lokacin zaɓen. Ya ambaci takamaiman laifuka kamar tsoratarwa, bibiyar mutane don cutarwa, sayen ƙuri’u, da sace akwatin zaɓe, inda ya yi gargaɗin cewa duk wanda aka kama da hannu a irin waɗannan ayyukan zai fuskanci hukunci a ƙarƙashin doka.
Ya kuma bayyana cewa za a samar da kotun tafi-da-ganka domin sauraron ƙararrakin da suka shafi mutanen da aka kama kan zargin tafka laifukan zaɓe.
Lokacin da aka tambaye shi game da cikakken bayani kan makaman da aka ƙwato daga hannun mutanen da ake zargi da ta’addanci a jihar, Iniedu ya ce har yanzu ƴansanda ba su tattara takamaiman bayanan makaman ba, amma zuwa yanzu sun ƙwato kusan haramtattun makamai 34, kuma ana ci gaba da bincike.