Ma’aikatan hukumar kayyade farashi da Sanya Ido kan Albarkatun Man Fetur (NUPRC) sun tsunduma yajin aiki na kan takaddamar horas da ma’aikata.
Ayyukan hukumar sun tsaya cak a fadin Najeriya, biyo bayan yajin aikin sai baba ta gani da ma’aikatan ta karkashin kungiyar (PENGASSAN) suka tsunduma.
Ma’aikatan sun tsunduma yajin aikin ne a ranar Litinin, wanda yanzu haka babban ofishin hukumar da ke Abuja ya kasance a rufe, koda yake rahotanni na nuni da cewa rufewar ta shafi sauran rassan ta na fadin kasarnan baki daya.
Kakakin hukumar Mista Eniola Akinkuotu, ya tabbatar da aukuwar lamarin, inda yace matakin da suka dauka ya gurgunta harkokin kula da sanya ido a bangaren hakar danyen mai da iskar gas na Najeriya.
“Gaskiya ne cewa wasu daga cikin ayyukanmu sun tsaya cak, sai dai muna tabbatar da cewa wannan bai shafi ayyukan da ake gudanarwa a matatun mai ko kuma hakar danyen mai gaba daya ba.” Inji Mista Eniola.
Ya kara da cewa yanzu ana kan tattaunawa tsakanin shugabannin hukumar da bangaren shugabannin kungiyar ma’aikatan domin samun daidaito.

Rahonni na nuni da cewa ma’aikatan suna nuna fushin su ne dangane da yadda hukumar ta sauya tsarin bayar da horo na musamman da ake basu a ciki da wajen kasarnan.
Sai dai wata majiya da ta nemi a sakaye sunanta, ta shaidawa Guardian cewa sauya tsarin horo na musamman da a baya akeyi a kasashen waje zuwa gida Najeriya ne ya haifar da rashin daidaito a tsakani.
A gefe guda, mahukuntan hukumar ta kayyade farashin mai (NUPRC) na kare matakin da cewa yin horon a cikin gida zai rage kashe kudade da bunkasa kwarewar a cikin gida.

A halin yanzu, ana gudanar da tattaunawa a matakin koli a Ofishin Mai baiwa Shugaban Kasa Shawara kan Tsaro Malam Nuhu Ribadu, bayan da bangarorin biyu suka kasa cimma dai-daito a tattaunawar farko.
Masana a harkar man fetur sun yi gargadin idan har yajin aikin ya tsawaita, zai iya sanyaya gwiwar masu zuba jari a fannin hakar danyen mai a Najeriya.
