Gwamnan Jihar Neja, Mohammed Umaru Bago, ya ce jam’iyyar APC a jihar na da burin samo wa Shugaba Bola Ahmed Tinubu sama da ƙuri’u miliyan biyu a zaɓen shugaban ƙasa na 2027.

Bago ya bayyana hakan ne yayin ƙaddamar da kwamitin yaƙin neman zaɓen shugaban ƙasa da na gwamnan jihar na APC mai mambobi 525, a Minna ranar Litinin.

Gwamnan ya ce jam’iyyar za ta yi amfani da tsarin tattara magoya baya daga rumfunan zaɓe zuwa matakin gundumomi, ƙananan hukumomi da jiha domin cimma wannan buri.

Ya bayyana cewa haɗin gwiwar siyasar da ke tallafa wa kamfen ɗin ta haura mambobi 100,000 a tsawon shekaru, abin da ya ce zai taimaka wajen shirya ayyukan yaƙin neman zaɓen jam’iyyar.

Bago ya kuma sanar da cewa za a ƙaddamar da ofishin yaƙin neman zaɓen shugaban ƙasa na APC a yankin Arewa ta Tsakiya da ke Minna a mako mai zuwa, inda ake sa ran manyan jami’an gwamnati da na jam’iyyar za su halarta.

By Bashar Muhammad Dange

Bashar Muhammad is a Nigerian multimedia journalist, broadcaster, producer, and Digital Manager at Blueprint Radio Hausa. He holds a B.Sc. and a Diploma in Mass Communication. He has experience in news reporting, radio production, digital media management, and content creation.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *